Kano: NNPP Ta Yi Rashi Bayan Ta Hannun Damar Kwankwaso Ta Yi Murabus Daga Mukaminta
- Ta hannun damar jigon siyasar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta yi murabus daga kujerar shugabar matan jami'yyar NPP
- Aisha Ahmed Kaita ta bayyana murabus din nata ne a yau Talata 2 ga watan Afrilu a birnin Kano a yankin Arewa maso Yamma
- Ta koka kan yadda aka yi watsi da magoya bayanta bayan ba da dukkan gudunmawa wurin kafa gwamnatin jihar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Shugabar matan jam'iyyar NNPP a Arewa maso Yamma, Aisha Ahmed Kaita ta yi murabus daga mukaminta.
Aisha Kaita ta ajiye aikin ne a yau Talata 2 ga watan Afrilu a birnin Kano saboda wasu dalilai, cewar Punch.
Musabbabin murabus din shugabar matan NNPP
Kaita ta ce ta yi murabus din ne a karan kanta kuma har yanzu ta na nan a mambar jami'yyar NNPP, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai ta koka kan yadda aka yi watsi da magoya bayanta wadanda suka ba da gudunmawa wurin kafa gwamnatin NNPP a jihar.
"Jiya na shaidawa Sanata Rabiu Kwankwaso kudiri na kan ajiye mukamin shugabar matan jam'iyyar NNPP a Arewa maso Yamma."
"Ya tambaye ni ko akwai matsala ne, na ce masa babu komai har yanzu ni mambar jami'yyar ce."
- Aisha Kaita
Kaita Tta ba da tabbacin kasancewarta 'yar NNPP
Ta tabbatar da cewa har yanzu ta na jam'iyyar NNPP kamar yadda ta sanarwa jigon jami'yyar, Sanata Rabiu Kwankwaso.
"Ni cikakkiyar 'yar Kwankwasiyya ce, ina tare da Kwankwasiyya tun a APC da PDP har zuwa NNPP."
- Aisha Ahmed Kaita
Aisha ta ce sun ba da gudunmawa mai karfi wurin kafa gwamnatin NNPP a Kano amma kuma ko neman shawarinsu ba a yi bare a zo maganan ba da mukamai a gwamnati.
An dakatar da shugabar matan APC
A baya, mun ruwaito muku cewa Jam'iyyar APC a jihar Kaduna ta dakatar da shugabar matan jam'iyyar, Maryam Suleiman.
Jam'iyyar ta dauki matakin ne saboda caccakar Gwamna Uba Sani da ta yi bayan ya yi zargin gadan bashi a jihar.
Wannan na zuwa ne bayan Maryam ta caccaki gwamnan Uba Sani ya yi katobara bayan zargin bashi da gwamnatin Nasir El-Rufai ta bari.
Asali: Legit.ng