An Yi Garkuwa da Matar Gwamnan PDP Bayan Musayar Wuta? Gaskiya Ta Bayyana

An Yi Garkuwa da Matar Gwamnan PDP Bayan Musayar Wuta? Gaskiya Ta Bayyana

  • Wani rubutu da aka wallafa a Facebook ya yi iƙirarin cewa an ɗauke uwar gidan gwamnan jihar Ribas, Lady Valerie Siminalayi Fubara
  • Rahoton ya nuna cewa sojoji ne suka sace matar gwamnan waɗanda ake zaton sun shiga rigimar da ke tsakanin Fubara da Nyesom Wike
  • Wani shafin binciken gaskiya ya gano ainihin abin da ya auku kuma ya wallafa rahoton ranar Talata, 26 ga watan Maris, 2024

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ribas - Wani rahoto da ke yawo a kafar sada zumunta Facebook ya yi iƙirarin cewa an yi musayar wuta tsakanin sojoji a Fatakwal, babban birnin Ribas.

Rahoton ya nuna cewa musayar wutar da auku ne tsakanin sojojin da ke goyon bayan Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas da magabacinsa, Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnan PDP ya naɗa tsohon shugaban tsageru a matsayin Sarki mai martaba

Valerie Fubara.
Ba a yi garkuwa da matar Fubara ba Hoto: Cloud Curve E-Media, Government House Media, Rivers State
Asali: Facebook

Legit Hausa ta tattaro cewa Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ba ya shiri da magajinsa Gwamna Simi Fubara, wanda rikicin ya ƙi ci kuma ya ƙi cinyewa har yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton wanda aka buga ranar 27 ga watan Fabrairu, 2024, ya yi iƙirarin cewa an yi artabu a Fatakwal, kuma yayin haka ne aka yi awon gaba da matar gwamna, Valerie.

A cewar rahoton:

"Arangamar da aka yi wanda ta shafe tsawon sa'o'i ta haddasa tashin hankali da damuwa kan yanayin tsaro a jihar.
"Ganau sun ce lamarin ya faru ne lokacin da ayarin motocin sojoji masu goyon bayan Wike suka haɗu da Gwamna Fubara da mai ɗakinsa a hanyarsu ta zuwa wani taro.
"Lamarin ya ƙara ƙamari ne lokacin da kowane ɓargare suka buɗe wuta, kuma hakan ya haddasa ruɗani da fargaba a kwaryar birnin.

Kara karanta wannan

Tsadar iskar gas: Jigon APC ya bukaci Shugaba Tinubu ya tausayawa talaka

Menene gaskiyar wannan ikirari?

A ranar Talata, 26 ga Maris, 2024, wani shafin binciken gaskiya, Africa Check, ya gudanar da bincike domin bankaɗo gaskiyar abin da ya faru.

Bayan binciken, kafar yada labaran ta bayyana cewa babu wata shaida da ke nuna faruwar lamarin.

Ta kuma kara da cewa babu wani sahihin rahoto na sace matar Fubara ma'ana dai labarin ƙarya ne.

Fubara ya ɗaga darajar tsohon shugaban tsageru

A wani rahoton kuma Gwamna Fubara ya ɗaga darajar tsohon shugaban tsageru zuwa matakin Sarki mai daraja ta farko a jihar Ribas.

Siminalayi Fubara ya mika takardar shaida da sandar mulki ga Amanyanabo na masarautar Okochiri, Sarki Ateke Michael Tom.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262