Ribadu, FFK zuwa Ningi: El-Rufai Ya Ruda APC, Ya Tada Kura Kwatsam a Siyasar Najeriya
Abuja - Nasir El-Rufai ya dawo gaban shafukan jaridu da gidajen talabijin bayan an rage jin duriyarsa a fagen siyasar Najeriya.
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Legit ta fahimci kwanan nan tsohon gwamnan na Kaduna ya dawo daga kasar Masar, daga dawowarsa ya jawo abin magana.
A rahoton nan, Legit ta tattaro jeringiyar ziyarce-ziyarce da Malam Nasir El-Rufai ya kai a ‘yan kwanakin nan da suka motsa kasa.
Su wa Nasir El-Rufai ya ziyarta?
1. Ribadu, jagororin APC da Nasir El-Rufai
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwanaki aka ji Mai ba Shugaban kasa shawara a harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da wasu jagororin APC sun ziyarci Nasir El-Rufai.
Sauran ‘yan tawagar da suka zauna da tsohon gwamnan na jihar Kaduna sun kunshi irinsu Kashim Ibrahim-Imam a birnin Abuja.
2. Nasir El-Rufai a sakatariyar SDP
A lokacin da ake rade-radin Nasir El-Rufai zai sauya-sheka ne, sai aka gan shi a sakatariyar jam’iyyar adawa ta SDP a birnin Abuja.
Muyiwa Adekeye ya shaidawa duniya cewa mai gidansa ya ziyarci shugaban SDP na kasa, Shehu Gabam ne a matsayinsu na abokai.
3. Abdul Ningi ya zauna da El-Rufai
Kwanaki bayan dakatar da Abdul Ningi daga majalisa saboda zargin cushe a kasafin kudi sai aka gan shi ya hadu da Nasir El-Rufai.
An fara yada jita-jita cewa Sanata Ningi zai hada-kai da Atiku Abubakar a kafa sabuwar jam'iyya, batun da aka karyata tuni.
4. Femi Fani Kayode da El-Rufai
Wata ziyara da ba da mamaki ita ce ta tsohon Ministan na harkar Abuja da tsohon abokinsa a gwamnatin tarayya, Femi Fani Kayode.
An ji Femi Fani Kayode yana jinjinawa Malam El-Rufai bayan zaman nasu. FFK yana cikin manyan abokan hamayya kafin dawowa APC.
El-Rufai ya ba yaronsa gudumuwa
Kwanaki kun ji labari Muhammad Bello El-Rufai ya yi bayanin gudumuwar da Malam Nasir El-Rufai ya ba shi da kamfen 2023.
Duniya ta ji yadda aka gamsar da tsohon Gwamnan Kaduna a kan yaransa ya fito takarar ‘dan majalisar wakilan tarayya a APC.
Asali: Legit.ng