Zai Yi Wahala APC Ta Kai Labari, Jiga-jigan Jam'iyya Sun Gargadi Tinubu Kan Halayen Ministansa
- Jiga-jigan jam'iyyar APC a birnin Tarayya, Abuja sun yi barazana ga Shugaba Bola Tinubu kan zabe mai zuwa na 2027
- Shugabannin jam'iyyar sun bukaci Tinubu ya ja kunnen Ministan Abuja, Nyesom Wike kan nuna wariya a mukamai
- Har ila yau, sun zargi Wike da fatali da 'ya'yan jam'iyyar da fifita 'yan jami'yyarsa ta PDP mai hamayya a mukamai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugabanninta jam'iyyar APC a Abuja sun yi Allah wadai da mukaman da Nyesom Wike ya nada.
Shugabannin suka ce Wike ya na kokarin cusa 'yan jami'yyarsa ta PDP a mukaman a madadinsu, cewar Thisday.
Menene APC ke kira ga Tinubu kan Wike?
Jiga-jigan jami'yyar sun bayyana haka ne a Abuja yayin ganawa da manema labarai a sakatariyar kungiyar 'yan jaridu (NUJ).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun bukaci Shugaba Tinubu ya gargadi Wike kafin ya lalata jam'iyyar a birnin Abuja musamman kan zaben 2027.
Jigon jami'yyar a Abuja, Abdulwahab Ekekhide shi ya bayyana haka inda ya ce an yi fatali da mambobin jami'yyar a birnin, cewar Leadership.
"Muna kira ga Shugaba Tinubu da ya gargadi Wike kan irin mukamai da ya ke naɗawa a birnin Abuja."
"Dole ya rinƙa ba 'yan jam'iyyar dama idan ba haka ba APC za ta iya rasa kason da ake bukata a zaben 2027."
- Abdulwahab Ekekhide
Dalilin gargadin APC ga Tinubu kan Wike
Wannan na zuwa ne bayan Wike ya nada Hon. Chidi Amadi a matsayin shugaban ma'aikatansa, cewar Liberty Radio.
Har ila yau, Shugaba Tinubu ya nada Hon. Felix Amaechi a matsayin kwadinetan hukumar gudanarwa ta birnin Abuja.
Wadannan nade-nade sun jawo cece-kuce musamman a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar APC da suka sha wahala wurin kawo gwamnatin Tinubu.
Wike ya gargadi makiyaya
Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya tura sakon gargadi ga makiyaya a birnin Abuja.
Wike ya ce ba zai lamunci yadda makiyaya ke kiwo kara zube a tsakiyar birnin ba wanda ke jawo matsaloli.
Asali: Legit.ng