Jam'iyyar PDP Ta Fadi Wadanda Ya Kamata a Ba Dama Su Saisaita Al'amura a Najeriya

Jam'iyyar PDP Ta Fadi Wadanda Ya Kamata a Ba Dama Su Saisaita Al'amura a Najeriya

  • Jam'iyyar adawa ta PDP ta fito ta gayawa duniya cewa maza sun gaza ya kamata a ba mata ragamar ƙasar nan
  • Shugaban jam'iyyar na ƙasa ya bayyana cewa na wannan zamanin sun gaza samar da ci gaban da ake so a ƙasar nan
  • Ambassada Umar Damagum ya yi nuni da cewa mata na taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaba a tsakanin al'umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta koka da yadda al’amura ke ci gaba da taɓarɓarewa a ƙasar nan, inda ta ce maza sun gaza don haka a ba mata dama.

Muƙaddashin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Ambassada Umar Damagum, shine ya bayyana hakan, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ana ba tsaro a kasa, Akpabio ya fito ya fadi ci gaban da Tinubu ya kawo a bangaren

PDP na so a ba mata dama
Jam'iyyar PDP na son a ba mata dama a Najeriya Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Facebook

Damagum ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a wajen bikin ranar mata ta duniya da kuma lacca da ofishin shugabar mata ta jam’iyyar PDP ta shirya, rahoton jaridar Independent ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muƙaddashin shugaban jam’iyyar ya ce a zamanin da, mata su ne ke warware duk wani saɓani da ake samu.

PDP na so a ba mata dama a Najeriya

Shugaban wanda ya samu wakilcin Sanata Samuel Anyanwu, sakataren jam’iyyar na ƙasa, ya yi nuni da cewa iyaye mata da mata na da matuƙar muhimmanci.

A kalamansa:

"Idan zai yiwu sannan ina addu'a da fatan cewa ko ba a lokacin mu ba, ina son wata rana na ga wata mace za ta shugabanci ƙasar nan. Kuma na faɗi hakan ne da gaske har cikin zuciyata, saboda zan iya gaya muku cewa mazan wannan zamanin sun gaza.

Kara karanta wannan

Shugabannin majalisa za su gana da Shugaba Tinubu, bayanai sun fito

"Hakan shi ne ya sanya waɗanda suka kafa PDP suka san rawar da mata ke takawa, shiyasa yanzu a Najeriya, duk ta yadda ka kalli abun, PDP ita ce jam'iyya mafi tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya ds Afirika."
"Wannan ita ce jam’iyya daya tilo da ke ba wa mata dama su yi takarar kowane muƙami kyauta ba tare da sayen fom ba. Muna yin hakan ne domin muna son ƙarfafa gwiwar mata.

Gwamnatin tarayya ta faɗi dalilin ƙarancin abinci

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta fito ta bayyana dalilin da ya sanya ake samun ƙarancin abinci a Najeriya.

Ministan noma, Abubakar Kyari ya bayyana cewa safarar kayan abinci da ake yi zuwa ƙasashe makwabta shi ne dalilin da ya sanya ake shiga halin ƙunci a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel