Ganduje Ya Dinke Ɓarakar da Ta Kunno Kai a APC, an Sauya Mataimakin Dan Takarar Gwamna

Ganduje Ya Dinke Ɓarakar da Ta Kunno Kai a APC, an Sauya Mataimakin Dan Takarar Gwamna

  • Shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya dinke wata ɓaraka da ta kunno kai a jami'yyar
  • Jam'iyyar ta yanke hukuncin nada Hon. Dennis Idahosa a matsayin mataimakin 'dan takarar gwamnan jihar Edo
  • Idahosa zai maye gurbin Hon. Omaregie Ogbeide-Ihama da aka zaba a makon da ya gabata domin a kawo maslaha

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - A karshe, jami'yyar APC ta zabi Hon. Dennis Idahosa a matsayin 'dan takarar mataimakin gwamnan jihar Edo a zaben da za a yi.

Wannan ya biyo bayan samun rikici bayan rashin nasara da Idahosa ya yi a zaben fitar da gwani da aka yi a jihar.

Kara karanta wannan

Malaman jami'a karkashin SSANU za su shiga yajin aiki, sun fadi yaushe za su dawo

Jam'iyyar APC ta sauya mataimakin ɗan takarar gwamnan jihar Edo
Jami'yyar APC ta sanar da sabon dan takarar mataimakin gwamna a Edo. Hoto: Hon. Monday Okpebholo, Hon. Dennis Idahosa.
Asali: Facebook

Rikicin APC: Matakin da Ganduje ya dauka

Shugaban APC, Abdullahi Ganduje da sakataren jam'iyya, Sanata Ajibola Bashiru za su gabatar da Idahosa ga Shugaba Tinubu a yau Litinin 18 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idahosa zai maye gurbin Hon. Omaregie Ogbeide-Ihama wanda dan takarar gwamnan ya sanar a makon jiya, a cewar The Nation.

Wannan na zuwa ne bayan doguwar ganawa a daren jiya Lahadi 17 ga watan Maris da shugabannin jam'iyyar da kuma mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.

Jiga-jigan da suka halarci taron APC

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai ɗan takarar gwamnan jihar, Hon. Monday Okpebholo da tsohon gwamnan jihar, Adams Oshiomole da kuma Hon. Dennis Idahosa.

Wannan na zuwa ne bayan Idahosa ya yi rashin nasara a zaben fitar da gwani da aka gudanar a ranar 1 ga watan Faburairu, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan PDP a Arewa ya kamu da son kujerar shugabancin jam'iyyar ta kasa, ya fadi dalillai

Zaben wanda ya ci karo da rikici daga bisani an sake gudanar da zaben a ranar 21 ga watan Faburairu.

An zabi dan takarar gwamnan Edo

A baya kun ji cewa jam'iyyar APC ta sanar da ɗan takarar gwamnan jihar da za a gudanar a Edo.

Hon. Dennis Idahosa ya samu nasarar kasancewa dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC.

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar a ranar 21 ga watan Satumbar wannan shekara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.