Na Hannun Daman Atiku Ya Fadi Nadamar da Ya Yi Kan Aiki da Tsohon Mataimakin Shugaban Kasan

Na Hannun Daman Atiku Ya Fadi Nadamar da Ya Yi Kan Aiki da Tsohon Mataimakin Shugaban Kasan

  • Daniel Bwala, tsohon mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku-Okowa, ya yi magana kan goyon bayan da yaba PDP a zaɓen 2023
  • Ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi kai tsaye a gidan talabijin, inda ya ce cewa bai yi nadamar goyon bayan jam’iyyar adawa ba
  • Lauyan ya ce ya amince da ƙaddararsa kuma ya yanke shawarar komawa jam’iyyar PDP a lokacin ne saboda ya yadda da hakan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Daniel Bwala, tsohon mai magana da yawun ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Atiku-Okowa, ya nanata cewa bai yi nadamar yin aiki da jam’iyyar PDP da ɗan takararta na shugaban ƙasa ba.

Kara karanta wannan

Kakakin kwamitin kamfen Atiku ya faɗi muhimman abubuwa 2 da Najeriya ke buƙata kafin zaɓen 2027

Ya kuma jaddada wajabcin tabbatar da an samar da tsaro a ƙasar nan kafin zuwan zaɓen shekarar 2027.

Bwala ya magantu kan goyon bayan Atiku
Bwala ya ce yanzu lokacin siyasa ya wuce Hoto: @BwalaDaniel
Asali: Twitter

Ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise tv a ranar Juma’a, 15 ga watan Maris, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Ban yi nadamar goyon bayan Atiku ba' - Bwala

A yayin da yake yabawa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan ƙoƙarinta, Bwala ya bayyana cewa bai yi nadama ba kan matakin da ya ɗauka na haɗa kai da Atiku Abubakar.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, ya bayyana cewa:

"Ban yi nadamar zuwa PDP ko goyon bayan Atiku ba, ina yin abubuwana ne bisa yadda da su kuma a ƙarshe idan har hakan bai yi nasara ba, na yarda da ƙaddara ta.
"Gaskiyar da na yarda da ita a yanzu ita ce, siyasa ta wuce, kuma saboda rikicin da ake fama da shi a Najeriya, hanya ɗaya tilo da za mu iya gudanar da zaɓen 2027 shi ne lokacin da Najeriya ta samu cikakken tsaro."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya jero mutanen da suka koma yaƙarsa saboda matakan da ya ɗauka a Najeriya

Me yasa Bwala ya zaɓi Tinubu akan Atiku

Ya bayyana cewa ya goyi bayan Tinubu ne saboda aƙidarsa ta siyasa ta haɗa kai da ƴan adawa don ciyar da ƙasar nan gaba.

A kalamansa:

"Na ga cewa wannan shugaban da nake goyon baya a APC yana ƙoƙarin ganin ya gyara kurakuran gwamnatin da ta gabata.
"Lokacin da ya ce yana son duk ƴan adawa su taru domin gina ƙasa, sai na ga lokaci ya yi da za a kalli makomar ƙasar maimakon siyasa. Dole ne a samu Najeriya kafin mu yi siyasa."

'Ku daina haɗa ni da Bwala' - Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar ya fito ya nuna cewa a daina haɗa shi da tsohon kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku/Okowa, Daniel Bwala.

Ya ce Bwala ba hadiminsa ba ne kuma ya yi aiki ne kawai a matsayin kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen, wanda tuni aikinsa ya ƙare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel