Kasashe 20 mafi karfin soji a duniya
Tsaro muhimmin abu ne a tarihin gwamnatin kasashen duniya. Hakan ne ya saka kasashe ke kasha makudan kudi a harkar tsaro, musamman bangaren aikin soja.
Duk da kasancewar kasashe na da hukumomin tsaro daban-daban da suke kokarin tabbatar da tsaro a ciki da wajen kasa, kasashen duniya sun fi bawa karfin soji muhimmanci a matsayin ma’auni na karfin tsaro na kasa.
Wajen fitar da alakaluman kasashe mafi karfin soji a duniya, masana kan yi la’akari da abubuwa da dama da suka hada da adadin sojin, fasahar zamani, makaman da suke amfani da su da wadanda suke dasu a ajiye da sauran su.
A wata kididdiga ta kasashe 20 mafi karfin soji a duniya da wata cibiyar nazarin karfin soji ta kasa da kasa (Global Power) ta fitar a 2017, ta ce kasar Amurka ce a mataki na daya a jerin kasashen. Sannan kasar Rasha ke biye da ita a mataki na biyu da kasar China a mataki na uku.
Ga jerin kasashen 20 kamar yadda Global Power ta fitar;
1. Kasar Amurka (US)
2. Rasha
3. China
4. India
5. France
6. Ingila (UK)
7. Japan
8. Turkey
9. Germany
10. Egypt
11. Italy
DUBA WANNAN: Sojojin sama sun rugurguza wasu gine-ginen Boko Haram a dajin Sambisa
12. South Korea
13. Pakistan
14. Indonesia
15. Israel
16. Vietnam
17. Brazil
18. Taiwan
19. Poland
20. Thailand
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng