2027: Atiku da Wasu Manyan Ƙusoshin APC Sun Fara Shirin Kafa Sabuwar Jam'iyya Domin Tunkarar Tinubu

2027: Atiku da Wasu Manyan Ƙusoshin APC Sun Fara Shirin Kafa Sabuwar Jam'iyya Domin Tunkarar Tinubu

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa da wasu manyan ƙusoshin APC sun fara shirin kafa sabuwar jam'iyyar siyasa gabanin 2027
  • Atiku, tsohon gwamnan Zamfara da Abdul Ningi suna cikin tawagar da mai yiwuwa za su yi kokarin maimaita abinda ya faru a 2013
  • An tattaro cewa Atiku ya fara tunanin matuƙar PDP ba ta ɗinke ɓarakarta ba, to ba zata kai labari ba a zaɓe na gaba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Wasu manyan kusoshin tsagin adawa a Najeriya na shirye-shiryen kafa sabuwar jam'iyyar siyasa domin kawar da APC a babban zaɓen 2027.

Wasu majiyoyi sun ce ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya fara kafa ginshikan sabuwar jam'iyyar tare da wasu ƴan majalisar tarayya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya naɗa tsohon shugaban PDP da wasu mutum 2 a manyan muƙamai

Atiku na jan ragamar kafa jam'iyya.
Ga dukkan. alamu Atiku bai haƙura da neman mulkin Najeriya ba Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Atiku ya damu da rigingimu da rashin haɗin kan PDP, yana tunanin idan ba ta sauya zani ba har 2027, jam'iyyar ba za ta iya samun galaba kan APC ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu sanatoci 2 na APC sun haɗa kai da Atiku

Wata majiya ta shaida wa jaridar The Nation cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya haɗa kai da tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, wanda ya nemi zama shugaban majalisar dattawa.

Mai yiwuwa a jawo shugaban kungiyar sanatocin Arewa, NSF), Abdul Ningi, domin ya yi duk mai yiwuwa wajen ganin shirin ya samu nasara a majalisa.

A cewar masu sharhi kan siyasa, ga dukkan alamu za a iya maimaita abin da ya faru a 2013, inda wasu gwamnoni da ‘yan majalisar tarayya suka yi wa PDP tawaye.

Yadda aka kafa APC a 2013

Kara karanta wannan

Atiku yayi maganar shirin 'ficewa' daga jam'iyyar PDP, ya ambaci laifin Shugaba Tinubu

Suka koma gefe suka haɗa kai da sauran jam'iyyun adawa wajen kafa All Progressives Congress (APC) a watan Fabrairu, 2023.

Jam'iyyun ANPP, CPC, ACN da tsagin APGA ne suka haɗu suka kafa jam'iyyar APC tare da mambobin tawagar da ya ɓalle daga PDP wacce ake kira da sabuwar PDP

Atiku, ɗaya daga cikin jagororin da suka kafa APC, ya sha kashi a zaben fitar da ɗan takarar shugaban kasa a 2014 a hannun Muhammadu Buhari.

Daga bisani ya koma jam’iyyar PDP inda ya kara da shugaban ƙasa na wancan lokacin, Muhammadu Buhari a zaɓen 2019, cewar rahoton The News.

A shekarar da ta gabata, Atiku ya sake shan kashi a hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Wane shiri Atiku ke yi domin lashe zaɓen 2027?

Majiyar ta ce tsohon mataimakin shugaban kasar da makusantansa na hangen za a iya maimaita abin da ya faru a 2013 wajen kafa sabuwar jam'iyya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fayyace gaskiya kan masu zargin Buhari ne ya lalata Najeriya

Ya ce:

"Shirye-shiryensu ya yi nisa, suna ganin kasar nan ta shiga yanayi irin wanda ta tsinci kanta a 2014 lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan."
"Wannan ya sa suka yanke shawarin kafa sabuwar jam'iyya domin kawar da mulkin APC a 2027."

Sai dai wani sanata daga kudancin Najeriya ya ce shi da takwarorinsa suna da masaniyar yunƙurin maida mulki Arewa idan suka yi nasarar kawo cikas da raunana gwamnatin Tinubu a 2027.

Tinubu ya gana da IBB a Minna

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu da tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida, sun yi wata ganawar sirri a Minna ranar Litinin.

Gwamna Muhammad Umar Bago na jihar Neja ne kaɗai ya shiga wurin da jiga-jigan biyu suka tattauna kan muhimmin batu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262