Atiku Yayi Maganar Shirin 'Ficewa' Daga Jam'iyyar PDP, Ya Ambaci Laifin Shugaba Tinubu

Atiku Yayi Maganar Shirin 'Ficewa' Daga Jam'iyyar PDP, Ya Ambaci Laifin Shugaba Tinubu

  • Atiku Abubakar ya fito ya yi magana kan batun cewa yana shirin tattara komatsansa ya fice daga jam'iyyar PDP
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana cewa ƴan amshin shatan Shugaba Tinubu ne ke yaɗa wannan jita-jitar
  • Ɗan takarar shugaban ƙasan a zaɓen 2023 ya kuma caccaki shugaban ƙasan kan watau Mai girma Bola Ahmed Tinubu
  • A cewar 'dan adawan, Tinubu ya fi mayar da hankali kan al'amuran siyasa fiye da na jagorancin al'ummar da ke karkashinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Atiku Abubakar ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya yi martani kan jita-jitar cewa yana shirin ficewa daga jam'iyyar PDP.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana rahoton a matsayin zuƙi ta malle.

Kara karanta wannan

"Ka da ka zama kamar Buhari": An ba Tinubu shawarar magance matsalar rashin tsaroS

Atiku ya magantu kan shirin barin PDP
Atiku ya musanta batun barin jam'iyyar PDP Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Wasu rahotanni dai da suka yi yawo sun bayyana cewa Atiku Abubakar na neman maimaita tarihi ta hanyar ƙauracewa jam'iyyar PDP kamar yadda ya yi a baya a shekarar 2013.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake mayar da martani kan rahoton a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X, babban jigo a jam'iyyar ta PDP ya bayyana cewa har yanzu yana nan daram a jam'iyyar, kuma ba ya tunanin ficewa daga cikinta.

Atiku ya bayyana masu yaɗa jita-jitar a matsayin ƴan amshin shatan Shugaba Bola Tinubu.

Atiku ya caccaki Shugaba Tinubu

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya caccaki shugaban ƙasa Bola Tinubu kan yadda ya yi watsi da harkokin mulki ya mayar da hankalinsa kan batun siyasar 2027.

Ya yi nuni da cewa abin takaici ne yadda shugaban ƙasan ya fifita al'amuran siyasa fiye da jin daɗin al'ummar da yake shugabanta.

Kara karanta wannan

2027: Atiku da wasu manyan ƙusoshin APC sun fara shirin kafa sabuwar jam'iyya domin tunkarar Tinubu

Ya buƙaci Tinubu da ya ajiye batun siyasa gefe guda, ya dawo ya mayar da hankali kan jin daɗin mutanen Najeriya da ke ƙarƙashin mulkinsa.

Dalilin Tinubu na tsoron Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani matashin ɗan siyasa masoyin Atiku Abubakar ya bayyana dalilin da ya Tinubu ke tsoron tsohon mataimakin shugaban ƙasan.

Adnan Mukhtar Adam ya bayyana cewa Atiku yana da ilmin tattalin arziƙi kuma yana da kuɗin da zai iya doke jam'iyya mai mulki a zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Online view pixel