Shugaba Tinubu Ya Iso Najeriya Bayan Shafe Kwanaki 2 a Ƙasar Larabawa, An Jero Ayyukan da Ya Yi

Shugaba Tinubu Ya Iso Najeriya Bayan Shafe Kwanaki 2 a Ƙasar Larabawa, An Jero Ayyukan da Ya Yi

  • Bola Ahmed Tinubu ya sauka a birnin tarayya Abuja yau Litinin, 4 ga watan Maris bayan kammala ziyarar kwana biyu a ƙasar Qatar
  • Shugaban ƙasar ya je wannan ziyara ne bisa gayyatar Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, kuma ya yi ayyuka da dama
  • Tinubu ya shaida rattaba hannu kan yarjejeniya daban-daban kuma ya halarci taron kasuwanci da zuba hannun jari tsakanin Najeriya da Qatar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dawo gida Najeriya bayan ziyarar kwanaki biyu da ya kai ƙasar Qatar.

Shugaban ƙasar ya kai ziyara ƙasar ne bisa gayyatar sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi abu 1 da za a yi wa masu neman cin hanci a gwamnatinsa

Shugaba Tinubu ya dawo Najeriya.
Shugaba Tinubu ya dawo Najeriya daga Qatar Hoto: Dolusegun16
Asali: Twitter

Bola Tinubu ya sauka a ɓangaren shugaban ƙasa na filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja da misalin karfe 6:37 na yamma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan ƙusoshin da suka tarbi Tinubu a Abuja

Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ne ya jagoranci jiga-jigan gwamnatin tarayya wajen tarbansa a filin sauka da tashin jiragen sama.

Sauran ƙusoshin da suka je tarbo Tinubu sun haɗa da shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike.

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da shugaban hukumar tsaron farin kaya (DSS), Yusuf Bichi, sun je wurin.

Wasu ayyuka Tinubu ya yi a Qatar?

A lokacin da yake Doha, babban birnin Qatar, shugaban ya tattauna da manyan hukumomin kasar karkashin jagorancin Sarki Sheikh Al Thani.

Haka nan kuma Shugaba Tinubu ya halarci taron yaukaƙa alaƙar kasuwanci da zuba hannun jari tsakanin Najeriya da Qatar, Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Ƴan Najeriya sun maida martani yayin da mataimakin Tinubu da manyan ministoci suka ziyarci Buhari

A yayin ganawar da aka yi tsakanin gwamnatin Najeriya da hukumomin Qatar, shugaba Tinubu ya shaida rattaba hannu kan yarjeniyoyi daban-daban.

Har ila yau, a yayin taron kasuwanci da zuba jari, Tinubu ya yi magana da 'yan kasuwar Qatar kan dimbin damammakin zuba jari da ake da su a Najeriya da riba mai gwaɓi.

Gwamnati za ta fara raba hatsi ga ƴan Najeriya

A wani rahoton kuma, ga dukkan alamu za a samu saukin wahalar da ake ciki yayin da gwamnatin tarayya ta ce za ta fara rabon kayan abinci a jihohin Najeriya.

Ministan noma da samar da isasshen abinci, Abubakar Kyari, ya ce za a bi matakan da suka dace wajen tabbatar da tallafin ya isa ga talakawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262