Kwankwaso ne yayi wa Ganduje riga da wando a siyasa – ‘Yar Baba Mataimaki
Wata ‘Yar Kwankwasiyya ta maidawa Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Ganduje martani kan kalaman sa game da jar hula da tsohon Gwamnan watau Rabiu Kwankwaso inda tace babu sulhu tsakani amma ya san zai yi nadama a 2019.
Jaridar Rariya ta rahoto cewa Wata Baiwar Allah mai suna Jamila Mohammad wanda aka fi sani da ‘Yar Baba Mataimaki da ja hankalin Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje inda tace ya tuna da abin da Kwankwaso yayi masa a siyasa.
Hajiya Jamila tace ta ji kalaman Gwamna Dr. Abdullahi Ganduje da abin da yake fada game da tsohon Gwamnan Kano Injiniya Rabiu Kwankwaso inda tace ya san cewa sai dai ya zama butulu don kuwa Kwankwaso yayi masa komai a rayuwa.
KU KARANTA: An kashe mutane wajen rikicinGwamna Ganduje da Kwankwaso
‘Yar Baba Mataimaki tace abin da mamaki ace a rasa irin sakayyar da Ganduje zai yi wa Kwankwaso bayan ya zama Gwamna shi ne yayi kokarin ganin bayan sa. Hajiya Jamila tace su ‘Yan Kwankwasiyya za su Ganduje ya cire jar hula.
Wannan ‘Yar Kwankwasiyyar tayi kira ga Gwamnan na Kano ya daina daukar shawaran su Abdullahi Abbas domin za su kai sa su baro sa. A karshe tace babu bukatar sulhu da ‘Yan Gandujiyya domin kuwa za su bata masu tarbiyya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng