Abin da Ya Sa Bola Tinubu da APC Suke Tsoron Atiku Abubakar a Takarar Shugaban Kasa
- Idan akwai wanda zai iya doke Bola Ahmed Tinubu idan an zo takara, wasu suna ganin wannan mutumi shi ne Atiku Abubakar
- Irinsu Adnan Mukhtar Adam Tudunwada sun bukaci jam’iyyar PDP ta tsaida Wazirin Adamawa sannan a mara masa baya
- Adnan ya fadawa Legit Atiku yana da ilmin tattalin arziki kuma yana da kudin yakin neman zabe a doke jam’iyya da ke mulki
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - Tun yanzu wasu sun fara buga gangar siyasa, ana ganin ya kamata a karbe mulki daga hannun Bola Ahmed Tinubu.
Kwamred Adnan Mukhtar Adam Tudunwada matashin ‘dan siyasa ne kuma wanda yake goyon bayan Alhaji Atiku Abubakar.
Atiku: Legit ta zanta da Adnan Tudunwada
Legit ta zanta da wannan ‘dan siyasa, inda ya shaida mata cewa Wazirin Adamawa shi ne ya fi dacewa da yin takara a 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da Atiku ya yi takara a 2019 da 2023 babu nasara ba, Adnan Mukhtar Adam Tudunwada yana so a sake ba sa tikiti.
Ko da jam’iyyar PDP ta tsaida wani ‘dan takara na dabam a 2027, Adnan Tudunwada ya ce da wahala ya iya doke Bola Tinubu.
"Shi ne mai karfi daga Arewa, shi kadai ne wanda a zahiri ta nuna yana da zuciya."
"Yana da arziki, babban ‘dan kasuwa ne kuma takarar kujerar shugaban kasa sai da kudi a Najeriya."
"Mun ga yadda aka yi da Muhammadu Buhari, sai da sauran ‘yan siyasa suka mara masa ya kai labari"
- Adnan Mukhtar Tudunwada
Adnan: "Atiku ya san tattalin arziki"
Tsohon ‘dan takaran kujerar majalisar dokokin yake cewa Atiku shi ne wanda kowa yake tsoro a APC saboda an san cancantarsa.
Baya ga haka, Adnan ya yabi gwaninsa da sanin tattalin arziki kamar yadda ya saba ba gwamnati mai-ci shawararin kawo gyara.
“Cigaba ne a rika daukar shawarar adawa kuma aka rika yin adawa da ilmi ta manufofi ba taba mutunci ba.”
- Adnan Mukhtar Tudunwada
Malamin makarantar ya ce Atiku ya fito da tsare-tsaren da zai bi kafin cire tallafin fetur, akasin garajen da shugaba Tinubu ya yi.
A cewar Adnan, za a samu mafita idan borin kunya bai hana a karbi shawarar Atiku ba.
Atiku Abubakar bai tsufa da takara ba?
Ana kukan Atiku zai yi tsufa da shugabanci a shekara 80, amma shi kuwa Adnan yana ganin an saba ganin dattawa a kan mulki.
A zantawarmu ya bada misali da shugabannin Amurka kamar Joe Biden da Donald Trump.
"Atiku yana da lafiya, ba shi da wata cuta a shekarun nan in ban da ciwo da ya ji a kafafunsa da yake mataimakin shugaban kasa."
- Adnan Mukhtar Tudunwada
An ce a LP da NNPP su bi Atiku a 2027
Idan zaben 2027 ya zo, kuna da labari Adnan Mukhtar Adam Tudunwada ya ce Atiku Abubakar ne mafita a kan sauran 'yan jam'iyyun adawa.
Matashin ‘dan adawan yana so jagororin Obidient da Kwankwasiyya su bi bayan jam’iyyar PDP domin gudun a raba kuri’u irin na 2023.
Asali: Legit.ng