Majalisa Ta Tsaida Lokacin da Za a Fito da Sabon Kundin Tsarin Mulki a Najeriya

Majalisa Ta Tsaida Lokacin da Za a Fito da Sabon Kundin Tsarin Mulki a Najeriya

  • An rantsar da wani kwamiti na musamman da zai gyara dokokin da ke cikin kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999
  • Mataimakin shugaban majalisar wakilai na kasa zai jagoranci aikin, ya yi alkawarin nan da shekaru biyu za su kammala
  • Hon. Benjamin Kalu yana so kudirin da aka gyara ya je gaban shugaban kasa kafin a fara shirye-shiryen babban zabe a 2027

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Mataimakin shugaban majalisar wakilan tarayya, Benjamin Kalu ya yi magana a kan aikin kwaskwarimar tsarin mulki.

A ranar Litinin, The Nation ta rahoto Hon. Benjamin Kalu yana cewa nan da watanni 24 za a gama aikin gyara kundin dokokin kasar.

Kara karanta wannan

Atiku ya karantar da Tinubu, ya fadawa Shugaban kasa hanyar gyara a saukake

'Yan majalisa
'Yan majalisa za su gyara tsarin mulki Hoto: House of Representatives
Asali: Facebook

Sabon kundin tsarin mulkin kasa

Da zarar gyare-gyaren sun kammala, za a kai kudirin gaban shugaban kasa ya sa hannu, wanda bayan nan sai zai zama sabuwar doka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ben Kalu ya shaidawa Najeriya wannan a lokacin rantsar da kwamitin majalisa da aka ba alhakin yi wa tsarin mulkin kasar garambawul.

Tsarin mulki: Tinubu zai sa hannu kafin 2027

Ana so kwamitin ya gama aiki, ya gabatar da gyare-gyaren ga shugaban kasa shekara guda kafin zabe saboda ya duba su da kyau.

Mataimakin shugaban majalisar ya nuna ana so ayi duk kwaskwarimar da za ayi wa kudirin kafin shekarar babban zabe ta gabato a 2027.

‘Yan majalisa suna canza dokokin kasar ne la’akari da cewa duniya tana canzawa har kullum, sai a kawo tsare-tsaren da ake bukata.

Gyara-gyaren da za a yi a tsarin mulki

An rahoto Hon. Kalu yana cewa an kawo masu bukatar kirkiro da ‘yan sanda a jihohi da na ba jihohi iko da ma’adanan da ke kasarsu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kafa kwamiti mai bangarori uku na ba shi shawara kan tattalin arziki

Daga cikin yunkurin da ake so akwai shigo da mata cikin harkokin siyasa sosai da fayyace kason da gwamnatoci ke karba daga haraji.

An kuma bukaci majalisar tarayya ta kawo dokar da za ta kirkiri magajin gari a birnin Abuja inda ake amfani da Ministoci a yanzu.

Kudirin da shugaban kasa ya maidawa majalisa

A baya an samu majalisa ta kawo kudiri amma shugaban Najeriya bai amince sun zama dokoki ba, wasu daga ciki sun dawo majalisar.

Idan wannan karo kudirin sun yi nasara, majalisar tarayya da na dokoki za su samu ikon aikawa shugaban kasa da gwamnoni sammaci.

Shugaban majalisa da jihohi

Ana ji labari babu wani Gwamna da ya fito ya ce da gaske ne an rabawa kowace jiha karin wasu N30bn, akasin zancen Godswill Akpabio.

Jami’an gwamnatoci sun tabbatar da cewa maganar shugaban majalisar dattawa na rabawa jihohi karin Naira Tiriliyan 1.08 karya ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng