Zaben 2027: Jigon PDP Ya Fayyace Gaskiya Kan Yiwuwar Yin Hadaka

Zaben 2027: Jigon PDP Ya Fayyace Gaskiya Kan Yiwuwar Yin Hadaka

  • Kiran haɗaka gabanin babban zaɓen 2027 ya kasance babban zance a fagen siyasar Najeriya
  • Wannan al’amari ya haifar da jam’iyyar APC, wacce ta ƙunshi jam’iyyun siyasa na haɗin gwiwa guda uku
  • Duk da wannan, akwai shawarwari kan jam’iyyar PDP da ta yi ta yi la’akari tare da bin irin wannan hanya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Ogun, Dr Segun Showunmi, ya bayyana ra’ayinsa kan shawarar jam’iyyar ta haɗa ƙarfi da ƙarfe da sauran jam'iyyun adawa a zaɓen 2027 mai zuwa.

Da yake zantawa da Legit.ng a wata hira ta musamman, mai neman shugabancin na PDP ya bayyana ra’ayinsa kan ganin jam’iyyar ta haɗe da wasu kafin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

APC ta shiga matsala yayin da dan takarar gwamna ya yi barazanar daukar mataki 1 a kanta

Showunmi ya yi magana kan hadaka
Showunmi ya nuna shakku kan yiwuwar yin hadaka a 2027 Hoto: Segun Showunmi
Asali: Twitter

Ya nuna damuwarsa cewa jam’iyyar na iya yin irin wannan dabarar da jam’iyyar APC ta yi a baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan takarar shugabancin PDP ya ce:

"Bari na gaya muku ta wannan hanyar. Na ɗaya ban ce ba mu son haɗaka ba. Kawai na ce ne ba zai yiwu ka yi amfani da hanya iri ɗaya da ta APC ba domin ƙwace mulki a hannunta.
"Kana ƙoƙarin bin hanyar da APC ta yi amfani da ita kuma ta ƙware a kanta. Na faɗi cewa haɗakar da suka yi ta buƙaci dukkanin jam'iyyun su kasance a ciki in banda sabuwar PDP.

PDP za ta ƙyale sunanta ta yi haɗaka?

Ya kuma bayyana cewa irin wannan mataki zai yi wuya, yana mai bayyana cewa shugabannin jam’iyyar PDP a kowane mataki ba za su yarda su bar suna, matsayinsu, da duk wani abu da ya haɗa jam’iyyar ba.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Edo: Manyan 'yan takara 3 daga APC, PDP da LP

A kalamansa:

"Sun manta da jam’iyyarsu ne suka fara sabuwar jam’iyya gaba ɗaya. Kuma ban ga yadda hakan zai yi wa PDP sauƙi ba.
"Shin PDP za ta ajiye sunanta, ta ajiye jam'iyyarta, waye zai bari su yi haka bayan kana da kusan gwamnoni 12 kp 13 da wasu sanatoci, ina jin wannan kawai wani mafarki ne."

Showunmi Ya Magantu Kan Takarar Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa Segun Showui ya yi magana kan batun sake shirin yin takarar shugaban ƙasa na Atiku Abubakar.

Tsohon ɗan takarar gwamnan na jam'iyyar PDP a jihar Ogun, ya bayyana cewa takarar Atiku ba matsala ba ce tun da shi ɗan Najeriya ne kuma ɗan jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng