Peter Obi Ya Fusata Ya Caccaki Hukumar INEC Kan Abu 1

Peter Obi Ya Fusata Ya Caccaki Hukumar INEC Kan Abu 1

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, ya yi martani kan rahoton da INEC ta fitar kan zaɓen 2023
  • Peter Obi ta hannun kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓensa, ya bayyana rahoton a matsayin babu ƙamshin gaskiya a cikinsa
  • Ya yi nuni da cewa uzurin da INEC ta kawo kan matsalar da na'urar IREV ta samu, ba abin da za a yarda da shi ba ne

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, ya zargi hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da yaudarar ƴan Najeriya kan rahoton zaɓen da aka fitar da safiyar Juma’a.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Ƴan sanda sun bayyana mummunan laifin da ya sa aka kama shugaban LP na ƙasa

A cikin rahoton zaɓen 2023 mai shafuka 526, wanda aka fitar a hukumance, INEC ta bayyana dalilin da ya sa na'urar IREV ta kasa saka sakamakon zaɓen shugaban ƙasa duk da cewa na'urar BVAS ta yi aiki ba tare da matsala ba.

Peter Obi ya caccaki INEC
INEC ta fitar da rahoto kan zaben 2023 Hoto: Mr Peter Obi
Asali: UGC

Hukumar ta alaƙanta ƙalubalen kan matsalar na'ura, amma duk da haka an warware ta, kuma hakan bai yi tasiri a kan sahihancin zaɓen ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Peter Obi ya ce kan rahoton INEC?

Obi wanda ya zanta da Daily Trust ta bakin Yunusa Tanko, babban mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen Obi-Datti, ya bayyana rahoton a matsayin magani bayan mutuwa.

A kalamansa:

"Ina jin rahoton na INEC magani ne bayan mutuwa. Maganar gaskiya ita ce, idan ba na nufin cewa da gaske INEC ta magance wannan batu kamar yadda ya faru a lokacin zaɓen ba, mai yiyuwa ne ƴan Najeriya sun yarda da kuma aminta da wannan rahoton.”

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Hukumar DSS ta gargadi kungiyoyin kwadago kan gudanar da zanga-zanga, ta fadi dalili

"Amma wajen mu, rahoton da hukumar INEC ta fitar da ke nuna cewa na'urar IREV ta ƙi yin aiki ko ɗora sakamakon a lokacin zaɓe ƙarya ne.
"Idan aka yi la’akari da cewa an yi zaɓuka uku wannan ranar, sai aka ɗora sakamakon zaɓen ƴan majalisar wakilai da majalisar dattawa ba tare da an samu matsala ba.
"Me ya sa za a samu matsala a na zaɓen shugaban ƙasa? Don haka gaba ɗaya a gare mu yaudara ne, raina jama’a da ƙoƙarin kawo rashin gaskiya."

Abin da LP Za Ta Kwace a Hannun PDP - Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya sake nanata matsayin jam'iyyar a siyasa Najeriya.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana cewa jam'iyyar ta shirya zama babbar jam'iyyar adawa a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng