Peter Obi Ya Yi Magana Kan Abu 1 da LP Za Ta Kwace a Hannun PDP

Peter Obi Ya Yi Magana Kan Abu 1 da LP Za Ta Kwace a Hannun PDP

  • Peter Obi na jam’iyyar Labour Party ya ce jam’iyyarsu ta daidaita da sabon matsayinta na babbar jam’iyyar adawa a Najeriya
  • Ana dai kallon PDP a matsayin babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, rawar da take takawa tun bayan da ta sha kaye a hannun APC a 2015
  • A cikin saƙonsa na sabuwar shekara, Obi ya yi addu'a ga Najeriya da ƴan Najeriya tare da rokon Allah ya biya musu buƙatunsu na ƙwarai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Awka, Anambra - Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a zaɓen 2023, ya tsayar da jam’iyyarsa a matsayin babbar jam’iyyar adawa a Najeriya.

Jam’iyyar PDP dai ta taka rawar jam'iyyar adawa tun bayan samun nasarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a shekarar 2015.

Kara karanta wannan

'Dan takarar gwamnan kuma sanata ya bayyana shirinsa na sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC

Peter ya ce LP za ta zama babbar jam'iyyar adawa
Peter Obi ya yi magana kan zaman jam'iyyar LP babbar jam'iyyar adawa a Najeriya Hoto: Peter Obi, PDP Nigeria
Asali: Twitter

A cikin saƙonsa na sabuwar shekara, tsohon gwamnan na jihar Anambra, ya ce jam’iyyarsa ta LP za ta cigaba da daidaita matsayinta na babbar jam’iyyar adawa a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Obi, jam’iyyar LP za ta tsaya tsayin daka a matsayinta na ƴar adawa da kuma cigaba da bin diddigin jam’iyyar APC mai mulki domin amfanin Nijeriya da ƴan Nijeriya.

Sabuwar Najeriya mai yiwuwa ce, in ji Peter Obi

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na twitter a ranar Litinin, 1 ga watan Janairu, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya ce burinsa da na magoya bayansa shi ne shugabanci nagari wanda aka shafe shekaru da yawa babu shi a ƙasar nan.

Duk da ƙalubalen, Obi ya cigaba da cewa samun sabuwar Najeriya mai yiwuwa ce.

Daga nan sai ya miƙa gaisuwarsa ga ɗaukacin ƴan Nijeriya tare da addu’ar Allah ya albarkace su da cika musu muradinsu a 2024 da kuma bayan nan.

Kara karanta wannan

Rikici ya kunno kai a APC bayan Ganduje ya caccaki jigon jam'iyyar kan shugabanci, bayanai sun fito

Jigon na LP ya bayyana cewa:

"Za mu cigaba da tattaunawa da ƙoƙarin da jam'iyyar LP ta yi domin daidaitawa da sabon matsayinmu na babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya. Za mu cigaba da haɗa kan dukkan ƴan Najeriya da abokanmu, waɗanda a yanzu sun fahimci babban tasirin hanyar da ba a ɗauka ba."

Sowore Ya Fadi Taimakon da Ya Yi Wa Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Omoyele Sowore ya bayyana wani sirrin Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen 2023.

Sowore ya bayyana cewa shi ne ya taimaka wajen fitowar Obi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party.

Asali: Legit.ng

Online view pixel