Edo 2024: Dirama Yayin da 'Dan Takarar APC Ya Dira a Ofishin Ganduje, Ya Gabatar da Bukata 1 Tak

Edo 2024: Dirama Yayin da 'Dan Takarar APC Ya Dira a Ofishin Ganduje, Ya Gabatar da Bukata 1 Tak

  • Mutanen jihar Edo na ganin dirama iri-iri daga bangaren 'yan siyasa gabannin zaben gwamna mai zuwa a jihar
  • Rikicin da ya dabaibaye manyan jam’iyyun siyasar jihar ya bazu ta ko’ina a sansanin ’yan siyasar APC da PDP kuma yana iya shafar sahihancin zaben na watan Satumba
  • Na baya-bayan nan shine 'dan takarar APC, Hon. Anamero Dekeri, wanda ya yi ikirarin lashe zaben fidda gwani na ranar Asabar sannan ya nemi Ganduje ya ba shi takardar cin zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Abuja - Daya daga cikin 'yan takarar jam'iyyar APC uku a zaben gwamna da za a yi a ranar 21 ga watan Satumba a jihar Edo, Hon. Anamero Dekeri, ya dira a babban sakatariyar jam'iyyar na kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Ganduje ya samu matsala a APC yayin da tsohon kwamishina ya fice daga jam'iyyar, ya fadi dalili

Hon Dekeri wanda ya isa sakatariyar a ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairu, ya bukaci shugaban jam'iyyar na kasa, Abdullahi Umar Ganduje da ya ba shi takardar shaidar cin zabe, rahoton Daily Trust.

Dan takarar APC ya nemi Ganduje ya ba shi takardar shaidar cin zabe
Edo 2024: Dirama Yayin da Dan Takarar APC Ya Dira a Ofishin Ganduje, Ya Gabatar da Bukata 1 Tak Hoto: Hon. Anamero Sunday Dekeri, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Ku tuna cewa zaben fidda gwani da aka yi a ranar Asabar ya samar da mutum uku da suka lashe zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kwamitin zaben fidda gwanin, Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo, ya sanar da Dennis Idahosa a matsayin wanda ya yi nasara.

Daga bisani kakakin baturen zabe na kananan hukumomi, Ojo Babatunde, ya ayyana Dekeri, a matsayin wanda ya lashe zaben.

Dekeri ya yi gaggawan zuwa ofishin Ganduje

A wani yunkuri na gaggawa, Dekeri, wanda ya isa sakatariyar APC na kasa a ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairu, ya isa ofishin Ganduje kai tsaye inda ya bukaci ya ba shi takardar shaidar cin zabe, rahoton Trust Radio.

Kara karanta wannan

‘Dan siyasa ya hakura da kujera, saboda magudi aka shirya domin ya lashe zaben majalisa

Dan majalisar ya yi ikirarin cewa shine ya samu adadi mafi rinjaye na kuri'un da aka kada a wajen zaben fidda gwanin.

Tsohon kwamishina ya bar APC a Edo

Legit Hausa ta rahoto a baya cewa bayan kammala zaɓen fidda gwani na gwamna, tsohon kwamishinan sadarwa da wayar da kan jama’a na jihar Edo, Andrew Emwanta, ya fice daga jam’iyyar APC.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, tsohon kwamishinan ya yi murabus ne saboda kura-kuran da aka samu a zaɓen fidda gwani na gwamna da aka gudanar a ranar Asabar, 17 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng