Wuya Ta Yi Wuya: Ma’aikatan APC Sun Fara Tunanin Shirya Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa
- Wasu daga cikin ma’aikatan jam’iyyar APC za su fito gaban duniya su yi zanga-zanga a dalilin tsada da wahalar rayuwa
- Ma’aikatan da ke babbar sakatariyar jam’iyya mai mulki a Abuja suna so a kara masu albashi kuma a rika biyansu alawus
- Rayuwa ta kara wahala musamman a garin Abuja saboda haka ma’aikatan suka hurowa shugabannin majalisar NWC wuta
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Ma’aikatan da ake biya albashi a bangarori da sassan hedikwatar jam’iyyar APC da ke garin Abuja sun koka da kuncin rayuwa.
Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa ma’aikatan jam’iyyar APC sun yi barazanar fitowa suyi zanga-zanga idan aka yi wasa da hakkokinsu.
Ganin halin kuncin rayuwa, hauhawar farashin kaya da tsadar abinci da ake fama da shi, ma’aikatan za su iya fitowa su shirya zanga-zanga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan APC za suyi zanga-zanga?
Ma’aikatan jam’iyyar ta APC suna so shugabannin da ke rike da jam’iyyar APC su biya su kudin gida da wasu sauran alawus da ya kamata.
Wani ma’aikaci da ya zanta da jaridar ba tare da ya bari an kama sunansa ba, ya zargi jagororinsu na jam’iyyar APC da barinsu a wahale.
Yayin da kananan ma’aikata su ke neman yadda za su rayu, wannan ma’aikaci ya ce shugabanni su na tashi da tulin albashi da alawus.
Ganduje yana biyan karin kudi a APC NWC
Amma dai wannan mutumi ya tabbatar da cewa a karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje, ana biyansu karin N35, 000 a wata.
Gwamnatin Najeriya tayi yarjejeniya da ‘yan kwadago cewa za a biya kowane ma’aikaci N35, 000 saboda rage radadin cire tallafin fetur.
Tsoron da ma’aikatan su ke yi shi ne daga Junairu watan Yunin 2024 za a biya wannan kudi, don haka suke so a kara masu albashi.
Shugabannin APC sun ki cewa uffan a kai
Da aka tuntubi Felix Morka a matsayin mai magana da yawun jam’iyya, sai ya ce sabanin cikin gida bai cikin abubuwan da ke gabansa.
Morka ya ce jam’iyyar APC tana fama da siyasar kasa da shirin zaben Edo ne a yanzu.
Manya a APC sun fara kuka da tattali
Mafi yawan mutane a yanzu suna kukan cewa rayuwa tayi matukar wahala. Ana da labari daga ciki har da Sanatoci da wasu manya a APC.
Sanata Muhammad Sani Musa ya fadawa gwamnati cewa tsare-tsarenta ba su aiki.
Asali: Legit.ng