Sarki a arewacin Najeriya ya ba Fulani makiyaya wa'adin kwanaki 30 su bar jiharsa
- Sarkin masarautar Muri a jihar Taraba ya ba Fulani makiyaya wa'adin barin jihar Taraba
- Sarkin ya koka kan yadda bata-gari cikin Fulanin ke addabar mutanen wasu sassan jihar
- Ya ce, dole ne su tattara su bar jihar ko kuma a tilasta musu barin ta ko sun so ko sun ki hakan
Sarkin masarautar Muri a jihar Taraba, Abbas Tafida ya ba da wa’adin kwanaki 30 ga makiyaya da ke addabar mazauna jihar kan su bar dazuzzukan fadin jihar ko kuma a tilasta musu yin hakan.
Gidan talabijin na Channels ta ce, Sarkin ya bayar da wa'adin ne a ranar Talata bayan sallar Idi.
Wannan ya biyo bayan yawaitar sace-sacen mutane, kashe-kashe, da hare-hare a jihar da wasu miyagu da ake zargin makiyaya ne ke aikatawa.
Ya yi ikirarin cewa Fulani makiyaya ne ke da alhakin aikata laifuka a jihar don haka ya kamata su bar dazuzzukan da ke cikin jihar cikin kwanaki 30 ko kuma a tilasta musu fita.
KARANTA WANNAN: Gwamna Zulum ya gwangwaje sojojin da suka ji rauni da miliyoyin Nairori ranar Sallah
Sarkin ya bukaci shugabannin Fulani Makiyaya da su fitar da bara-gurbi a tsakanin su.
PM News ta ruwaito Sarkin na cewa:
“Fulaninmu makiyaya a dazuzzuka, kun shigo wannan jihar ne kuma mun karbe ku, me ya sa za ku zo garuruwa da kauyuka don satar mutane, har ma da fyade ga matanmu?
“Saboda wannan barazanar da ta ki karewa, an ba kowane Bafulatani makiyayi a wannan jihar kwanaki talatin ya bar cikin dazuzzuka.
"Mun gaji da rashin bacci ba dare ba rana, kuma yunwa kadai a cikin kasar nan na da girman da ba za mu bari ta ci gaba ba."
Jihar Taraba da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya na fuskantar munanan ayyukan ta'addanci kama daga satar mutane zuwa hare-haren 'yan bindiga.
Jigon APC a Zamfara ya yi kira da a kori tsohon Gwamna Yari da Marafa
Wani jigon jam'iyyar All Progressive Congress, APC, a jihar Zamfara, Abdullahi Shinkafi ya nuna bacin ransa game da matakin da tsohon gwamna Abdul'azeez Yari da Sanata Kabiru Marafa suka dauka kwanan nan game da shawarar kwamitin rikon jam'iyyar na kasa.
Shugabannin jam'iyyar na kasa a lokacin sauya shekar gwamna Bello Matawalle da sauran mambobin jam'iyyar sun rusa majalisar zartarwar APC a Zamfara tare da ayyana gwamnan a matsayin shugaban jam'iyyar a jihar, in ji gidan talabijin na TVC.
KARANTA WANNAN: Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa
Gwamna Zulum ya gwangwaje sojojin da suka ji rauni da miliyoyin Nairori ranar Sallah
A wani labarin, Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bai wa sojojin da suka ji rauni da ke yaki a yankin tallafin naira miliyan 10 a jiya Talata.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya sanar da ba da tallafin ne a yayin liyafar cin abincin rana da babban hafsan sojin kasa na Najeriya Manjo Janar Farouk Yahaya ya shirya a Barikin Maimalari da ke Maiduguri.
Gwamna Zulum ya yaba wa dakarun kan jajircewarsu da kuma jaddada alkawarin gwamnatinsa na ci gaba da ba su goyon baya har a cimma nasara a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya a yankin.
Asali: Legit.ng