Rikici Ya Barke a Jam’iyyar Labour, Ana Zargin Julius Abure Ya Karkatar da Naira Biliyan 3.5
- Ma'ajin jam'iyyar Labour ta kasa, Misis Oluchi Oparah ya nemi shugaban jam'iyyar na kasa ya ba da ba'asin yadda ya kashe kudaden jam'iyyar
- Misis Oparah na zargin cewa Mista Julius Abure, ya karkatar da akalla naira biliyan 3.5 na kudin fom din takara da jam'iyyar ta samu a 2023
- Oparah ta ce Abure ya ci karensa ba babbaka matsayin shugaban jam'iyyar amma yanzu lokaci ya yi da zai girbi abin da ya shuka
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Sabon rikici ya barke a jam’iyyar Labour Party (LP) yayin da Misis. Oluchi Oparah ta bukaci Julius Abure, shugaban jam’iyyar na kasa da ya ba da ba'asin yadda ya kashe kudaden jam’iyyar.
Kudaden sun haura sama da naira biliyan 3.5, wanda aka samu daga siyar da fom da sauran ayyukan tara kudade domin zaben 2023 da ya gabata, The Nation ta ruwaito.
Oparah, wadda take ma’ajin kudin jam'iyyar ta kasa ta bayyana bukatar hakan ne a yayin ganawa da manema labarai a Abuja a ranar Litinin, 12 ga watan Fabrairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta bayyana cewa tun bayan kammala zaben shekarar 2023, shugaban ya ki daukar kwararan matakai na yin binciken yadda aka tafiyar da kudaden jam’iyyar.
Oparah na zargin Abure ya karkatar da kudin jam'iyyar
Oparah ta ce:
"Ya zama tilas in fito fili in yiwa ‘yan jarida jawabi game da ayyukan almundahana da suka dabaibaye jam’iyyarmu a karkashin jagorancin Mista Julius Abure, shugabanta na kasa na yanzu.
“A matsayina na ma’ajin jam'iiyar na kasa, na tsaya a gabanku domin in nemi Mista Abure ya fito ya yi mana bayani kan laifin cin zarafin ofis da kuma karkatar da kudaden jam’iyya."
Oparah ta kara da cewa Mista Abure ya ci karensa ba babbaka, kuma da gangan ya wofantar da karfin ikon kujerata kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada.
Isa Yuguda ya tona asirin masu hannu a faduwar darajar Naira
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Bauchi, Mallam Isa Yuguda ya tona asirin wadanda ke da hannu a faduwar darajar Naira.
Isa Yuguda ya ce gurbatattun'yan siyasa da ke boye daloli a gidajensu da bankunan kasashen waje ne sanadin faduwar darajar Naira.
Ya kuma bayyana cewa Najeriya ba za ta fita daga matsalar karancin abinci ba har sai an kawo karshen matsalolin tsaro da ke hana manoma yin wadataccen noma a kasar.
Asali: Legit.ng