‘Dan Takara Ya Fallasa Komai, ‘Yan Siyasa Na Amfani da Addini Domin Mulkin Filato
- Nentawe Yilwatda ya ce a tarihin Filato, an dade ana amfani da siyasar addini domin cin ma manufa
- ‘Dan takaran na APC a zaben 2023 yana ganin cewa da gangan aka yi masa tabo da alaka da musulunci
- Duk ‘dan siyasar da aka likawa tambarin zama ‘dan takaran musulmai bai kai labari a zaben Filato
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Plateau - Nentawe Yilwatda wanda ya yi wa APC takarar gwamna a jihar Filato, ya tona asirin abokan aikinsa watau ‘yan siyasa.
Nentawe Yilwatda ya zargi ‘yan siyasar Filato da amfani da addini saboda manufar siyasa da mulki, Daily Trust ta kawo rahoton.
Musulmi da kiristoci a Filato
‘Dan siyasar yake cewa a jihar, idan ana so a bata sunan ‘dan takara, sai a alakanta shi da addinin musulunci domin tika shi da kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yilwatda wanda ya yi harin zama gwamna bayan hukuncin kotu yake cewa mafi yawan lokuta sharri ake yi wa masu neman mulki.
‘Dan takaran ya yi hira da manema labarai a garin Jos, inda aka ji ta bakinsa bayan kotun koli ta tabbatar da zaben Caleb Mutfwang.
Yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida, Yilwatda ya ce da gan-gan ake alakanta shi da jam’iyyarsa ta APC da addinin musulunci.
Tarihin siyasar addini a Filato
Ba wannan ne karon farko a tarihin Filato da aka jefi wani da kusanci da musulmai saboda ya tsaya neman mukami ba a cewar Yilwatda.
A zaben 1983, haka aka yi wa John Kadiya na cocin ECWA, aka ce shi ne ‘dan takaran musulmai da zai gwabza da Marigayi Solomon Lar.
Duk da kusancinsa da cocin ECWA kuma dattijo a cikin kiristoci, ‘dan takaran na zaben 2023 ya ce haka aka yi wa Kadiya bakin fenti.
A 1991 Fidelis Tapgun ya yi takara da Bagudu Hirse, aka ce Hirse yana tare da musulmai.
Irin wannan shaida Yilwatda ya ce an yi wa David Jang da yake ANPP a 2003 da Pauline Tallen a 2011 haka zalika Simon Lalong a APC.
Malaman musulunci da kiristoci sun hadu
Ana da labari kungiyar Jama’atu Nasrul Islam ta ce hauhawan farashin kayayyakin abinci zai iya birkita kasar nan, dole a dauki mataki.
Haka kuma aka ji wata kungiyar kiristoci tayi addu’o’i a Kudancin Najeriya, ta nemi gwamnatin Bola Tinubu ta ceto al’umma daga yunwa.
Asali: Legit.ng