Tsadar Rayuwa: Sheikh Jingir Ya Fadi Matsayarsa Kan Zaban Tikitin Musulmi da Musulmi, Ya Yi Gargadi

Tsadar Rayuwa: Sheikh Jingir Ya Fadi Matsayarsa Kan Zaban Tikitin Musulmi da Musulmi, Ya Yi Gargadi

  • Shugaban kungiyar Izalar Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce ba zai taba yin dana sanin zaban tikitin Musulmi da Musulmi ba
  • Jingir ya ce duk masu jiran ya yi nadamar zaban Tinubu za su yi ta jira har abada a banza don ba zai taba yi ba
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wasu mazauna Gombe kan wannan martani Sheikh Jingir a zabe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau – Fitaccen Malamin addini, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi magana kan zaban tikitin Musulmi da Musulmi.

Shugaban kungiyar Izalar Jos ya ce duk masu jiran ya yi nadamar zaban Tinubu za su yi ta jira har abada, cewar Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kaduna ya fadi abu guda 1 tak da zai kawo karshen rashin tsaro a Arewa

Jingir ya yi magana kan tikitin Musulmi da Musulmi a halin da ake ciki
Sheikh Jingir ya ce bai yi dana sanin zaben Tinubu ba. Hoto: Sheikh Sani Yahaya Jingir.
Asali: Facebook

Martanin Sheikh Jingir kan zaben Tinubu

Jingir ya bayyana haka ne yayin da ya ke jawabi ga jama’a a wani faifan bidiyo inda ya caccaki masu zaginsa da cewa ya goyi bayan Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da ya ke martani kan tsadar rayuwa da ake ciki, Jingir ya ce bai taba dana sanin zaban tikitin ba amma dai ba shi ya ce tinubu ya yi haka ba.

Ya ce dukkan masu zaginsa kan haka munafukai ne da yawa ma ba Tinubu suka zaba ba.

Ya kara da cewa shi ya bukaci Tinubu ya yi adalci bai ce ya yi haka ba inda ya ce ba zai taba dana sanin zabar Musulmi da Musulmi ba.

Jingir ya ce bai yi dana sani ba

Ya ce:

“Wadanda ke zagina kan tikitin Musulmi da Musulmi makaryata ne, ba su zabi Tinubu ba.

Kara karanta wannan

Girman rawani na ya fi karfin yan bindiga su sace ni ko hallaka ni, Fitaccen Basarake ya yi alfahari

“Su na cewa Tinubu zai dauke Abuja zuwa Legas, ni na shawarci Tinubu ya yi hakan?.
“Na zabi tikitin Musulmi da Musulmi kuma na fadawa Tinubu ya yi adalci, na yi masa addu’ar samun lafiya da nasara a zabe kuma ya samu.”

Jingir ya ce Musulman kasar su na son Kiristoci inda ya ce ko kaso daya na Kiristoci ba su zabi tikitin Musulmi da Musulmi ba.

Ya kara da cewa:

“Na rantse da Allah na zabi Tinubu don addinin Musulunci saboda Allah kuma ubangiji ya umarce mu da mu yi adalci har wadanda ba Musulmai ba.
“Duk mai jiran na yi dana sani zai dade ya na jira, zan sake zaban Musulmi da Musulmi a duniya ko da ina gargarar mutuwa.”

Legit Hausa ta ji ta bakin wasu kan lamarin:

Wani dan agajin Izala tsagin Sheikh Jingir da ya boye sunansa ya ce maganar da malam ya fada gaskiya ne Musulunci shi ne gaba.

Kara karanta wannan

Neman tabarraki: Shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya, Ali Nuhu ya ziyarci Sarkin Kano

Ya ce:

"Ni banga kuskure a maganar malam ba kawai mutane ne sun rasa abin fadi suke hucewa a kansa.

Har ila yau, Abubakar Isa ya ce wannan ra'ayin malam ne kuma ya na da zabin hakan amma shi babu mai sake dora shi a harkar siyasa.

Umar Faruk wanda ke tsagin malam ya ce:

"Tabbas malam ya na da gaskiya a maganarsa idan har mutum don Allah ka zabe shi babu dana sani.

Jingir ya yi murabus kan harin Kaduna

Kun ji cewa Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi Allah wadai da harin bam a jihar Kaduna.

Jingir ya bukaci a yi bincike tare da hukunta wadanda ke da hannu a cikin harin da ya hallaka Musulmai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel