Raunin APC Ya Fara Fitowa, Shugaban Karamar Hukuma Ya Dawo NNPP a Kano
- Auwalu Lawan Aranposu zai canza gida a siyasa, zai kulla aure da jam’iyyar NNPP mai rike da Kano
- Shugaban karamar hukumar ta Nasarawa ya dade da kafarsa daya a wajen APC da ta ba shi mulki
- Wani na kusa da Rabiu Kwankwaso ya tabbatarwa Legit da cewa a makon nan za a karbi Aranposu
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - Auwalu Lawan Aranposu wanda shi ne shugaban karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano zai sauya-sheka.
Labari ya zo wa Legit cewa Hon. Auwalu Lawan Aranposu zai fice daga jam’iyyar APC zuwa NNPP mai mulki a jihar Kano.
Auwalu Lawan Aranposu zai tafi NNPP?
Ibrahim Adam wanda hadimi ne ga Rabiu Musa Kwankwaso ya shaida mana wannan bayan jin Abdullahi Ramat ya sauka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A safiyar Talata, Auwalu Lawan Aranposu ya fito Facebook ya nunawa duniya cewa zai koma NNPP mai alamar kayan marmari.
Shugaban karamar hukumar ya ce ungulu ta koma gidanta na tsamiya, a bayaninsa kuma ya ce Abba Yusuf yana kaunar talakawa
Sai dai magoya bayan shugaban karamar hukumar suna ta yawo da hotunansa a gidan gwamnati tare da Abba Kabir Yusuf.
Yaushe Auwalu Lawan Aranposu zai bar APC?
Majiyarmu ta ce a ranar Larabar nan za a gabatar da Auwalu Lawan Aranposu a matsayin cikakken ‘dan jam’iyyar NNPP.
Tun tuni take-taken Hon. Aranposu su ke nuna yana neman ya yi hannun riga da APC da ta ba shi damar samun mulki a 2021.
NNPP za ta ji dadin shigowa Aranposu a Kano
Ibrahim Adam ya shaidawa Legit suna maraba da wannan sauya-sheka domin kuwa hakan zai karawa NNPP yawan mabiya.
"Shugaban karamar hukuma ne mai-ci, kuma idan dai wanda ke mulki zai shigo jam’iyyarmu, cigaba aka samu domin zai zo ne da magoya bayansa."
"Nasara ce ga NNPP sannan jam’iyyar APC tayi rashi. ‘Yan siyasa mu na neman jama’a ne har kullum domin mu kara karfi."
"Daga yanzu zuwa 2027, za a birne siyasar Gandujiyya a Kano."
- Ibrahim Adam
Rigimar Aranposu da APC a Kano
‘Dan siyasar ya zargi Nasiru Yusuf Gawuna da kin goyon bayansa a lokacin da za a shiga zaben shugabannin kananan hukumomi.
Aranposu wanda ya yi karatu a Kano Poly da jami'ar ABU Zariya yana ganin tun farko NNPP ta doke APC mai-ci a zabukan 2023.
Ungulu da kan zabo a siyasa
Ko a lokacin da APC ta ke sa ran karbe mulki da ake shari’ar zabe, ‘dan siyasar yana da ra’ayin cewa yaudarar magoya baya ake yi.
Hon. Auwal Aranposu yana cikin 'yan siyasar da suka rika juyawa jam'iyyarsu baya.
.
Asali: Legit.ng