Zaben Cike Gurbi: Ƴan Sanda Sun Yi Caraf da Ƴan Daba a Kano, An Fadi Wanda Ya Ɗauko Hayarsu

Zaben Cike Gurbi: Ƴan Sanda Sun Yi Caraf da Ƴan Daba a Kano, An Fadi Wanda Ya Ɗauko Hayarsu

  • Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi caraf da wasu ƴan daba masu shirin hargitsi a zaɓen cike gurbi da ake a jihar
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar wanda ya tabbatar da kamun ya bayyana cewa an kama ƴan daban ne ɗauke da makamai
  • Kwamishinan ya yi nuni da cewa ƴan daban sun bayyana cewa wani ɗan siyasa ne ya ɗauko hayarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Rundunar ƴan sandan jihar Kano a ranar Asabar ta tabbatar da cafke wasu ƴan daba da ake zargi an ɗauƙo hayarsu domin kawo cikas a zaɓen cike gurbi da ake gudanarwa a ƙaramar hukumar Kunchi ta jihar.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Usaini Gumel, wanda bai bayyana adadin mutanen da aka kama ba a lokacin da yake zantawa da manema labarai, ya ce ƴan daban da aka kama suna ɗauke da makamai, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

An tsaurara matakan tsaro a rumfuna yayin da mutane suka fito zaben ƴan majalisa 3 a Kano

Yan sanda sun yi kamu a Kano
Yan sanda sun kama yan daba a Kano Hoto: Kano State Police Command
Asali: Facebook

A cewarsa, an yi zargin wani ɗan siyasa ne da ya tsaya takara a zaɓen ya ɗauko waɗanda ake zargin aiki, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ina aka cafke ƴan daban?

A kalamansa:

"An kama ƴan daban ne a yankin Kunchi/Tsanyawa, ɗaya daga cikin mazaɓun da ake sake zaɓe a jihar.
"Mun ga wata babbar mota da ta samu matsala a gefen hanya. Mun ga mutane da yawa a gefen hanya. Da farko sun nuna mana cewa man fetur ɗin motar ne ya ƙare. Amma da muka lura sosai, mun ga suna ɗauke da makamai.
"Wani Abdulrazaq Muhammad wanda aka fi sani da Mai Salati daga Kano Municipal ya shaida mana wani mutum da ke takara a yankin ya gayyace su.
"Za mu gano mutumin ko da gaske ɗan takara ne a zaɓen da kuma dalilin da ya sa ya gayyace su yankin.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An bankado babban sanata mai daukar nauyin ta'addanci a Arewa

"Muna zargin suna cikin daji ne domin yi wa jami’an zaɓe kwanton ɓauna yayin da suke kan hanyarsu ɗauke da sakamakon zaɓe."

INEC Ta Dakatar da Zaɓen Cike Gurbi a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta dakatar da zaben cike gurbin da ake yi a wasu mazabun jihohin Kano, Enugu da Akwa Ibom.

INEC ta bayyana cewa ta ɗauki wannan matakin ne saboda tashe-tashen hankula, tafka kura-kurai da kuma garkuwa da wasu jami'an zaɓe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel