Kano: Hukumar INEC Ta Dauki Mataki Kan Matsalar Kawo Tarnaki a Zabe, Bayanai Sun Fito

Kano: Hukumar INEC Ta Dauki Mataki Kan Matsalar Kawo Tarnaki a Zabe, Bayanai Sun Fito

  • Hukumar zabe ta INEC ta bayyana fara bincike kan samun matsaloli a rumfunan zabe a jihohi uku
  • Hukumar ta ce an samu matsalolin da suka hada da ta da tarzoma da kuma sace da kuma tarwatsa zaben
  • Hukumar ta dakatar da dukkan zabukan a wasu mazabun da suka hada da Kano da Enugu da Akwa Ibom

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta ce ta fara binciken kawo hargitsi yayin zabukan cike gurbi a Kano.

Hukumar ta ce ta samu rahoton ta da husuma da neman kawo cikas a zaben cike gurbin da ake gudanarwa.

An samu hargitsi a zabukan cike gurbi a jihar Kano
Hukumar INEC ta fara binciken rikici a zabukan cike gurbi. Hoto: Mahmud Yakubu, INEC.
Asali: Getty Images

Jihohin da aka samu hargitsi a zaben

Kara karanta wannan

Kano: A karshe, kotu ta dauki mataki kan Danbilki Kwamanda da zargin neman ta da husuma

Jihohin da hukumar ta tabbatar da cewa an samu hargitsin sun hada da Kano da Akwa Ibom da Enugu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yau Asabar ce 3 ga watan Faburairu aje gudanar da zaben cike gurbi a mazabu 8.934 da ke jihohi 26 na kasar.

Hukumar ta bayyana haka ne a yau Asabar 3 ga watan Faburairu a shafinta na X inda ta ke ba da bayanai kan yadda zabukan ke tafiya.

Hukumar ta sanar da soke zaben a dukkan mazabun da aka lissafo da suka hada da Kunchi/Tsanyawa da ke jihar Kano.

Har ila yau, ta ce ta na bibiyar dukkan bayanan samun matsaloli musamman daga 'yan daban siyasa da kuma sace akwatunan zabe.

A jihar Kano, an samu matsalolin kawo hargitsi a mazabar Kunchi/ Tsanyawa da ke karamar hukumar Kunci a jihar, cewar Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Murna ta koma ciki bayan kotu da datse dan PDP shiga takarar Sanata saura kwanaki 2 zabe

Martanin hukumar zaben kan matsalar

Sanarwar ta ce:

"A mazabar Kunchi/Tsanyawa da ke jihar Kano, an samu rahoton kawo tarnaki a zaben da ya shafi rumfuna 10 a karamar hukumar Kunchi.
"Yayin da a jihar Enugu aka samu matsala a mazabar Enugu ta Kudu a Majalisar jihar wanda ya shafi rumfuna takwas.
"A jihar Akwa Ibom kuwa, an samu matsala a mazabar Ikono/Ini da ke jihar inda rumfuna 2 suka fuskanci matsalolin ta da husuma."

An cire PDP a zaben cike gurbi

Kun ji cewa hukumar zabe ta cire tambarin jam'iyyar PDP a takardar dangwala zaben cike gurbi a jihar Plateau.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis 1 ga watan Faburairu yayin shirye-shiryen gudanar da zaben cike gurbi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel