Korarren Kakakin Majalisa da Mataimakinsa Sun Dawo Kan Kujerunsu a Jihar Arewa, Bayanai Sun Fito
- Korarren kakakin Majalisar jihar Bauchi ya samu damar dawowa kan kujerarsa bayan sake zabe a mazabar Ningi
- Abubakar Suleiman na jam’iyyar PDP a samu nasarar ce bayan samun kuri’u 11,785 a zaben da aka gudanar
- Ha rila yau, hukumar INEC ta ce dan takarar APC, Khalid Captain Ningi ya samu kuri’u 10,339 inda ya kasance na biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bauchi – Tsohon kakakin Majalisar jihar Bauchi, Abubakar Suleiman ya sake dawowa kan kujerarsa bayan nasara a zabe.
Suleiman ya samu nasarar ce a zaben da aka gudanar a jiya Asabar 3 ga watan Faburairu a mazabar Ningi a jihar.
Mene Hukumar INEC ta ce kan zaben?
Yayin da ya ke sanar da sakamakon, Farfesa Ahmed Abdulhamid ya ce Suleiman na jam’iyyar PDP shi ne ya yi nasara a zaben.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ahmed ya ce dan takarar ta PDP ya samu kuri’u 11,785 yayin da dan takarar APC, Khalid Captain ya samu kuri’u 10,339.
Idan ba a mantaba, Kotun Daukaka Kara ta rusa zaben kakakin Majalisar inda ta bukaci sake zabe a wasu rumfuna, TheCable ta tattaro.
Kotun ta umarci sake zaben ne a mazabu 10 a mazabar Ningi bayan dan takarar APC ya kalubalanci zaben.
Sauran sakamakon zaben da aka sanar
Har ila yau, Tsohon mataimakin kakakin Majalisar jihar, Jamilu Dahiru shi ma ya samu nasara a zaben mazabar Bauchi ta Tsakiya.
Yayin sanar da sakamakon zaben, Baturen zaben, Farfesa Isma’il Shehu ya tabbatar da Jamilu na jam’iyyar PDP wanda ya yi nasara.
Ya ce:
“Jamily Umaru Shehu ya samu kuri’u 45,240 yayin da ya doke abokin hamayyarsa, Aliyu Abdullahi Illelah na APC wanda ya samu kuri’u 40,266.
The Nation ta tattaro cewa jam’iyar PDP a jihar ta lashe dukkan zabukan da aka gudanar a kujeru hudu a jihar.
Wuraren da aka gudanar da zaben a Majalisar jihar sun hada da Bauchi da Zungur/Galambi da Ningi da kuma Madara/Chinade.
NNPP ta ci zabe a Kano
Kun ji cewa hukumar zabe ta INEC ta sanar da sakamakon zaben cike gurbi a jihar Kano.
Hukumar ta ayyana Bello Butu-Butu na jam’iyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Rimin Gado/Tofa.
Asali: Legit.ng