Zaben Cike Gurbi: Mutane Miliyan 4.6 Za Su Zabi Madadin Gbaja, Umahi da Sauransu

Zaben Cike Gurbi: Mutane Miliyan 4.6 Za Su Zabi Madadin Gbaja, Umahi da Sauransu

  • Hukumar zaben Najeriya ta fitar da kididdigan masu kada kuri'a a zaben da ake yi a ranar Asabar 3 ga watan Fabrairu
  • A cewar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), masu kada kuri’a miliyan 4.6 ne za su zabi dan takarar da suke so
  • Hukumar ta kuma bayyana cewa za a gudanar da zaben ne a kananan hukumomi 80 a fadin jihohi 26

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Mutane 4,613,291 da suka mallaki katunan zabe ne za su kada kuri’u a zabukan cike gurbi da za a yi a fadin Najeriya.

Ana gudanar da zaben ne domin cike gurbi a majalisun tarayya da na jihohi sakamakon mutuwa ko murabus din mambobi.

Kara karanta wannan

INEC ta dakatar da zaɓen cike gurbin da ake yi a Kano da wasu jihohi 2, ta jero dalilai

Ana gudanar zaben cike gurbi
Zaben Cike Gurbi: Mutane Miliyan 4.6 Za Su Canja Makomar Gbaja, Umahi da Sauransu Hoto: Pius Utomi Ekpei
Asali: Getty Images

Kotun sauraren kararrakin zabe ta ba da umarnin sake gudanar da zabe a wasu mazabu ko rumfunan zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu zabe sun shirya tsaf domin kada kuri’u a fadin jihohi 26, ciki harda tara da za su bayyana makomar sanatoci biyu, yan majalisar wakilai hudu, da yan majalisar jihohi uku.

Kididdigar INEC kan zaben fidda gwani

Shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa zaben zai cike guraben sanatoci uku, yan majalisar tarayya 17 da na jiha 28 a fadin kananan hukumomi 80.

Wannan ya shafi yankuna masu rajista 575 da kuma rumfunan zabe 8,934, tare da masu rajista 4,904,627 da kuma katuna 4,613,291 da aka karba.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, jihohin da abun ya shafa sun hada da Ebonyi, Yobe, Kebbi, Lagos, Ondo, Taraba, Benue, Borno, Kaduna, Plateau, Akwa Ibom, Anambra, Cross River.

Kara karanta wannan

Kano: Hukumar INEC ta dauki mataki kan matsalar kawo tarnaki a zabe, bayanai sun fito

Sauran sune Delta, Enugu, Jigawa, Katsina, Adamawa, Bauchi, Bayelsa, Kano, Nasarawa, Niger, Oyo, Sokoto, da Zamfara.

Wasu manyan kujeru ne ke kasuwa?

Fitattun kujerun da ba kowa sun hada da na shugaban ma’aikatan shugaban kasa Bola Tinubu, Femi Gbajabiamila; Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi.

Sauran sune na Sanata Ibrahim Geidam; Olubunmi Tunji-Ojo, da Tanko Sununu, wadanda suka yi murabus bayan nada su a gwamnati mai ci.

Isma’ila Maihanchi, zababben dan majalisar wakilai daga jihar Taraba, ya rasu kafin kaddamar da majalisar dokoki ta kasa, kuma Abdulkadir Danbuga daga Sokoto ya rasu a watan Oktoban 2023.

'Yan Najeriya sun yi muhawara kan Kwankwaso da El-Rufai

A wani labari na daban, mun ji cewa wani mai amfani da dandalin soshiyal midiya, @A_Y_Rafindadi, ya haifar da zazzafan muhawara a soshiyal midiya da hasashensa kan Nasir El-Rufai da Rabiu Musa Kankwaso.

Matashin ya bayyana cewa tsohon gwamnan na jihar Kaduna, El-Rufai ya fi tsohon gwamnan Kano, Kwankwaso, jagoran 'yan Kwankwasiyya farin jini a kujerar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel