An Shiga Rudani a Jos Bayan Hukumar INEC Ta Cire Sunan PDP a Zaben Cike Gurbi, APC da LP Sun Shiga

An Shiga Rudani a Jos Bayan Hukumar INEC Ta Cire Sunan PDP a Zaben Cike Gurbi, APC da LP Sun Shiga

  • An samu hargitsi bayan cire tambarin jam’iyyar PDP a jikin takardar dangwala zabe da hukumar INEC ta rarraba
  • Matsalar ta faru ne lokacin da ake rarraba kayayyakin zaben a Jos na jihar a yau Alhamis 1 ga watan Faburairu
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani dan a mutun jam'iyyar PDP kan wannan lamari da INEC ta yi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau – An shiga tashin hankali bayan cire tambarin jam’iyyar PDP da hukumar zabe ta yi a jihar Plateau.

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zaben cike gurbin a ranar 3 ga watan Faburairu, cewar Channels TV.

Babu tambarin PDP a takardun dangwala zaben jihar Plateau
An shiga hayaniya bayan cire sunan PDP zaben cike gurbi. Hoto: Caleb Mutfwang.
Asali: Facebook

Mene ke faruwa da PDP a Plateau?

Kara karanta wannan

Murna ta koma ciki bayan kotu da datse dan PDP shiga takarar Sanata saura kwanaki 2 zabe

An gano matsalar ce lokacin da ake rarraba kayayyakin zaben a birnin Jos na jihar a yau Alhamis 1 ga watan Faburairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar IPAC ta soki matakin hukumar zaben na cire jam’iyyar PDP wanda ta kwatanta a matsayin abin takaici kuma ba za a amince da hakan ba.

Shugaban hukumar INEC da ke kula da jihohin Plateau da Kaduna da Nasarawa, Mohammed Kudu ya na bankin CBN shiyyar Jos don raba kayayyakin.

Zabukan cike gurbin da za a yi sun kunshi kananan hukumomi shida da ke fadin jihar baki daya, cewar Daily Times.

Akwai alamun da gan-gan aka cire PDP

Kananan hukumomin sun hada da Bassa da Barikin-Ladi da Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da Jos ta Gabas da kuma Riyom.

An rarraba kayayyakin ne gaban wakilan jam'iyyu da 'yan jaridu da masu saka ido da jami'an tsaro, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Bayan sha da kyar a Kotun Koli, Gwamnan Arewa ya dage zaben ciyamomi kan dalili 1, bayanai sun fito

Ana cikin haka ne aka gano babu tambarin PDP a jikin takardar dangwala zaben sai dai kuma akwai na APC da PRP da LP.

Lamarin ya jawo hayaniya yayin da magoya bayan PDP ke zargin INEC da bijirewa umarnin kotu da ta ce ko wace jami'yya za ta shiga zaben.

A jiya ne magoya bayan jam'iyyar a Jos suka fito zanga-zanga don neman sanin ko akwai sunan PDP a zaben.

Legit Hausa ta tattauna da wani dan jam'iyyar PDP a Jos, Muhammad Sani Ahmed kan wannan lamari.

Sani ya ce daman an yi hasashen hakan zai faru tun kafin ranar fara rabon kayayyakin a Jos.

Ya ce:

"Dalilin haka ne ma ya sa 'yan jam'iyyar PDP suka fito zanga-zanga a ranar Alhamis don sanin makomar jam'iyyar a zaben."

PDP ta nada shugabar mata

Kun ji cewa jamiyyar PDP a Nigeria ta nada Hon. Amina Arong a matsayin sabuwar shugabar mata a jam'iyyar.

Wannan na zuwa ne bayan rasuwar Farfesa Stella da ke rike da kujerar a watan Oktobar 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel