Fetur Zai Iya Kara Tsada Maimakon a Samu Sauki da Matatun Gida Za Su Fara Aiki

Fetur Zai Iya Kara Tsada Maimakon a Samu Sauki da Matatun Gida Za Su Fara Aiki

  • Gwamnatin tarayya ta nanata cewa an kusa kammala gyaran matatar mai da ke garin Fatakwal a Ribas
  • Idan an gama komai, za a iya tace gangunan danyen mai 60, 000 a rana, amma ba dole farashi ya sauka ba
  • ‘Yan kasuwa suna zargin har yau ana biyan tallafin man fetur wajen shigo da mai, lamarin zai iya canzawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa an fara gwajin tace danyen mai a matatar mai da ke garin Fatakwal a jihar Ribas.

A wajen wani taro da aka yi da manema labarai, Punch ta ce ‘yan kasuwa suna tsoron cewa farashin man fetur zai tashi sama.

Man fetur
Bola Tinubu ya cire tallafin fetur Hoto: Getty Images, The News
Asali: Getty Images

Dala zai sa fetur ya kara tsada

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da fusatattun matasa suka kona gidan babban basarake, an yi karin bayani

Abin da ya sa ‘yan kasuwa suke wannan hasashe shi ne ganin yadda darajar Dalar Amurka ta lula a kan Naira ‘yan kwanakin nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan mutum yana neman Dala a kasuwar canji, sai ya kashe kusan N1500 a yau, wannan zai jawo fetur ya kara tsada a gidan mai.

Legit ta rahoto cewa ko a bankuna an saida kowace Dala a kan kusan N850 a makon nan.

Alkawarin tace mai a Fatakwal

Da zarar an gama gwajin matatar, gwamnatin tarayya ta ce za a samu kaya a kasuwa. Kwanaki 40 kenan da yin alkawarin nan.

Abin da hakan yake nufi shi ne matatun da ke cikin gida za su kawo saukin shigo da fetur, dizil da man jirgi da ake yi daga kasar waje.

Karamin ministan harkokin fetur, Heineken Lokpobiri ya shaidawa manema labarai halin da ake ciki a matatar da ke garin Fatakwal.

Kara karanta wannan

Mai gadin makaranta a Kano ya dauki ransa a cikin aji saboda tsohuwar matarsa ta sake aure

Fetur: Ba a fara tace mai ba har yau

Lokpobiri ya ce an gama wani bangare na gyaran da ake yi, amma ba a cika alkawarin da aka dauka na fara tace danyen mai ba.

A Disamba, Ministan ya sha alwashi zuwa bayan bikin kirismeti matatar za ta fara tace ganguna 60, 000 a kowace rana ta duniya.

Da aka tambaye shi game da halin da ake ciki, ya shaida cewa sai da ya tambayi shugaban matatar abin da ya jawo bacin lokacin.

Yadda za a karya Dala a kasuwa

An ji labari idan gwamnatin Bola Tinubu ta rasa yadda za a magance tashin Dala, Reno Omokri ya kawo shawarar farfado da Naira.

Mukarrabin tsohon shugaban kasa ya kira sunayen wasu da yake ganin sun taimaka wajen karya Naira saboda matsayinsu a NCC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng