Jigon PDP Ya Aikawa Irinsu Atiku Sako, Ya Fadi Wanda Za a Tsaida Takara a 2027

Jigon PDP Ya Aikawa Irinsu Atiku Sako, Ya Fadi Wanda Za a Tsaida Takara a 2027

  • Bode George ya fadawa kusoshin da ke PDP su ajiye maganar sake dauko ‘dan takaran shugaban kasa daga yankin Arewa
  • A zabukan da aka yi a 2019 da 2023, jam’iyyar PDP ta ba Atiku Abubakar tuta ne, daga Kudu aka nemo ‘dan takaran mataimaki
  • George ya ce a zaben 2027 ba za ta sabu ba, babu wanda zai nemi tikitin jam’iyyar PDP sai mutumin yankin kudancin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Bode George tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP ne a Najeriya, ya fara magana game da takarar da za ayi a 2027.

Cif Bode George ya kira taron manema labarai, inda The Cable ta ce ya soki masu kokari tikitin PDP ya tsaya a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Duk wani ‘Dan majalisar dokokin da ya koma APC a Ribas ya rasa kujerarsa – PDP

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Bode George, Atiku Abubakar
Cif Bode George, Shugaban kasa da Atiku Abubakar Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Bode George, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

'Yan Arewa su hakura da takarar 2027 a PDP

‘Dan siyasar ya ce dole idan zaben 2027 ya zo, jam’iyyar PDP ta tsaida ‘dan takaranta na shugaban kasa daga yankin Kudancin kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi a garin Legas a ranar Litinin, ‘dan siyasar ya fadawa abokansa na Arewa cewa su hakura da batun yin takara a 2027.

2027: Jigon PDP ya kira taron 'yan jarida

A taron manema labaran da ya shirya, jagoran na PDP ya ce za a kai jam’iyyarsu gidan tarihi idan dai ba a dauki shawararsa ba.

Amma duk da adawa da takarar mutumin Arewa, George ya kara da cewa babban abokinsa daga yankin ya fito, bai da matsala da su.

“Ina so in gargadi wasu jiga-jigai a babbar jam’iyyarmu ta PDP, idan ba ayi da gaske ba, jam’iyyar nan za ta shiga bolar tarihi a 2027.

Kara karanta wannan

Wike v Fubara: Asalin dalilin ‘Yan majalisan Ribas na dawowa APC Inji Jagororin Jam’iyya

Kwandon tarihi suna ne da ake kiran kungiya, jama’a ko wani wanda ya yi fice a baya, amma ya rushe saboda dalilai da za a iya gyarawa."

- Bode George

Daily Trust ta rahoto George ya na cewa PDP za ta zama tsohon labari idan ba a gyara ba, ya ce dole mutanen Arewa su hakura da takara.

PDP: Arewa ko Kudu za a kai takara a 2027?

"Mutumin Arewa ba zai iya zama ‘dan takaranmu na zaben shugaban kasa a takarar 2027 ba, maganar ke nan kurum.
Daga yanzu har 2031, ka da wani ya nemi tikitin jam’iyyarmu daga yankin Arewa."

- Bode George

Cif George wanda ya yaki takarar Atiku Abubakar a zaben 2023 tun yanzu ya fara nuna zai marawa mutanen yankin Kudu baya ne a 2027.

Kalubalen Atiku a zaben 2027

Kwanakin baya aka ji labari tsohon hadimin ‘dan takaran 2027 ya warwar abin da ya sa 'yan PDP ba su tare da Atiku Abubakar a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Takarar 2023: Abin da Ya Taimaki Tinubu Kan Amaechi, Osinbajo da Lawan Inji Jagoran APC

A wata hira da aka yi da babban 'dan siyasar, Umar Ardo ya bayyana cewa Atiku Abubakar yana da jan aiki sosai a gaban shi a cikin PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng