Masoya Sun Fara Zugo Peter Obi, Za Su Jawo Masa Matsala a Mulkin Tinubu

Masoya Sun Fara Zugo Peter Obi, Za Su Jawo Masa Matsala a Mulkin Tinubu

  • Halin da aka shiga ya tunzura wasu har ta kai suna kawo shawarar ayi zanga-zanga a fadin Najeriya
  • A irin na su tunanin, zanga-zangar lumuna za ta sa shugabannin kasar nan su dawo cikin hayyacisu
  • Peter Obi ake so ya shiga gaba ayi zanga-zangar kamar yadda aka yi wa gwamnatin PDP a 2012

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Wasu magoya bayan Peter Obi, sun gaji da yadda abubuwa su ke tafiya tun bayan hawan Bola Ahmed Tinubu mulki.

An samu wasu daga cikin mabiya ‘dan takaran na LP a zaben 2023 da suke ganin ya kamata a fara shirya zanga-zanga a kasar.

Peter Obi
Magoya bayan Peter Obi suna so ayi zanga-zanga Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Prophet Switch ya yi amfani da shafin X inda ya yi kira ga ‘dan takaran shugaban kasar da ya jagoranci a shirya zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Iyali ba abin wasa ba: Mijin Layla ya dauki mummunan mataki a kan Sadiya Marshall

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jama’a suna ta irin wadannan maganganu tun da aka ji yadda Naira ta ke karyewa a kowace rana, a yau ta doshi $1 ta N1, 500.

Kira na musamman ga Peter Obi

"Ya Peter Obi,
Don Allah ka jagoranci zanga-zanga.
Duk abin da zai faru, sai dai ya faru.
Ba za ta yiwu mu cigaba a haka ba.
Muna bukatar zanga-zanga a fadin kasar.
Abin ya isa haka nan"

- Prophet Switch

Peter Obi zai saurari kiraye-kirayen jama'a?

Masu wannan kira sun rabu inda wasu ke ganin idan aka yi zanga-zangar lumana, za a ja hankalin gwamnatin Bola Tinubu.

Switch ya ce da irin wannan yunkuri aka fara har jam’iyyun adawa suka ga bayan gwamnatin Goodluck Jonathan a 2015.

A gefe guda kuwa wasu na ganin hakan zai iya zama tarko, a cafke fitaccen ‘dan siyasar da zargin neman tada kayar baya.

Kara karanta wannan

CBN: Duk da ana ta surutu, ma’aikata 1500 da ke Abuja za su fara aiki a Legas

LP da Obi su shiryawa 2027

Wadanda suke ganin zanga-zanga ba za tayi wani tasiri ba, sun ba magoya bayan Obi shawarar su fara shiryawa zaben 2027.

Da ya nemi mulki a bara, tsohon gwamnan ya zo bayan jam'iyyun APC ne da PDP.

Wani mai suna Olawale Bakare yana ganin hakan ba za ta yiwu domin wadanda ke cikin gwamnati duk mutanen Peter Obi ne.

Irinsu Kwara State Prophet Elisha kuwa sun ce Allah ya raka taki gona, domin sai wanda ya koshi ne zai iya fita zanga-zanga.

“Masu miliyoyin Dala su fara zanga-zanga domin talakawa ba su iya sayen shinkafa.”

- Kwara State Prophet Elisha

Tashin Dala a mulkin Tinubu

A halin yanzu ana da labarin yadda ake fuskantar matsanancin tashin kudin kaya a kasuwa musamman farashin abinci.

Darajar Naira ta karye tun da sabon gwamnan bankin CBN ya bar farashin Dalar Amurka a hannun ‘yan kasuwa tun a bara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng