Iyali ba Abin Wasa Ba: Mijin Layla Ya Dauki Mummunan Mataki a Kan Sadiya Marshall

Iyali ba Abin Wasa Ba: Mijin Layla Ya Dauki Mummunan Mataki a Kan Sadiya Marshall

  • Yusuf Adamu Gagdi ya fito dandalin X ya yi magana a karonsa na farko a game da Sadiya Marshall
  • Ba tare da kama suna ba, an fahimci ‘dan majalisar tarayya ya bada umarni an tsare kawar matarsa
  • A wani bidiyo, Sadiya Marshall ta jefi kawarta da laifuffuka iri-iri, Hon. Gagdi yace ba zai zura ido ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Yusuf Adamu Gagdi ya dauki mataki a kan wata Sadiya Marshall wanda ake zargi ta bata sunan mai dakinsa, Layla Ali Othman.

‘Dan majalisar tarayyan ya yi maganganu da-dama a dandalin X jim kadan bayan taya sahibarsa murnar cika shekara 38 da haihuwa.

Sadiya Marshall ta tsoka mai gidan Layla Othman Ali
Sadiya Marshall ta tsoka mai gidan Layla Othman Ali Hoto: Hon. Yusuf Adam Gagdi
Asali: Facebook

Yusuf Adamu Gagdi yace an tsare Sadiya Marshall

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya fara shirin murabus daga muƙaminsa don yin takara? Gaskiya ta bayyana

Hon. Yusuf Adamu Gagdi ya shaidawa mabiyansa a shafinsa matar da tayi bidiyo a kan mai dakinsa, tana hannun jami’an tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Gagdi, idan Sadiya Marshall ta ji matsa, za ta fito da hujjojin da ta ke ikirarin tana da su a kan zargin da take yi wa matarsa.

Muddin ta gagara fito da hujjojin, ‘dan siyasar yace wannan mata za ta dawo ta karyata kanta kamar yadda ta jefi Layla da zargi.

Kalaman Yusuf Adamu Gagdi

"Ku tambayi inda ta ke a yanzu… za ta sake yin magana da bakinta, ta janye kalaman da tayi a kan matata…."
"Ba zai yiwu ta kasance a tsare na kwanaki biyu kuma ya zama ba ta fito da hujjojin da ta ke ikirari kan matatata ba."
Ka rike kalamai na, zan tabbata ta je gidan yari idan ba ta fito da bidiyoyi, hotuna, sakonni da faifen muryan mai dakina ba"

Kara karanta wannan

Mai Gidan Layla Othman ya zabi aika mata sako gaban duniya ana tsakiyar runtsi

- Yusuf Adamu Gagdi

Gagdi ya bugi kirji yana cewa ba da wani da ke daure ba, babu wata hujja da za a fito da ita na amayarsa da wani mahaluki a ban kasa.

Da ya cigaba da magana a kafar sadarwan zamanin, ‘dan majalisar na APC yace sai da a fadi duk abin da za a fada, dole ya kare matarsa.

Legit ta lura jigon na APC a jihar Filato ya tanka har masu maganar mai dakinsa ta canza suna ko ta rage, yace ba a sabawa addini ba.

"Matana (iyalina) ba abin wasa ba ne ga kowa."

- Yusuf Adamu Gagdi

Layla Ali Othman ta cika 38

Jiya ne ranar zagayowar lokacin haihuwar fitacciyar ‘yar kasuwa, Hajiya Layla Ali Othman, an ji mai gidanta ya aika mata sako.

A shekarar bara 'yar kasuwar ta auri Hon. Gagdi mai wakiltar mutanen Pankshin/Kanke/Kanam a majalisar wakilan tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel