‘Ba Tinubu Bane Zabin Allah’: Peter Obi Ya Yi Martani Mai Zafi Ga Kalaman Aisha Buhari

‘Ba Tinubu Bane Zabin Allah’: Peter Obi Ya Yi Martani Mai Zafi Ga Kalaman Aisha Buhari

  • Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi ya ce ba Tinubu bane zabin Allah kamar yadda ake fadi
  • A cewarsa, bai kamata a yi amfani da sunan Allah a lamari mai kama da barna ba ko kuma nasarar murdiya
  • Bayan nasarar Tinubu, Aisha Buhari da sauran ‘yan APC sun dage cewa, Allah ne ya zabi Tinubu ya gaji Buhari

Najeriya - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi a ranar Litinin ya yi martani ga kalaman mambobin APC da ke cewa, Bola Ahmad Tinubu ne zabin Allah ga ‘yan Najeriya.

Idan baku manta ba, uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta siffanta nasarar Bola Ahmad Tinubu na APC da tsarin da Allah ya yi, kuma ya kamata ‘yan Najeriya su karbi hakan, kamar yadda Ripples Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare: An Fallasa Ɗan Takarar Shugaban Kasan da Peter Obi Ya Yi Wa Aiki a Zaɓen 2023

Hakazalika, ta ce tana da yakinin Tinubu ba zai yaudari ‘yan Najeriya ba, kuma tabbas zai tafi da mata da matasa a mulkinsa.

Ba Tinubu bane zabin Allah, inji Obi
Bola Ahmad Tinubu, zababben shugaban Najeriya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Martanin Peter Obi

Sai dai, da yake matrani ga bayanin Aisha Buhari a wata tattaunawa da Arise Tv, Obi ya ce bai dace uwar gidan shugaban kasa ta ce Tinubu ne zabin Allah ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, Allah yana goyon bayan gaskiya da bin daidai ne ba wai sabanin haka ba kamar yadda aka gani a zaben da ya gabata, rahoton Tribune Online.

Da aka tambaye shi ko zai amince da nasarar Tinubu a matsayin nufin Allah kamar yadda wasu malaman addini ke ikrari, Obi ya ce:

“Abin da suke da’awa a kai ba komai bane face matsala ga Najeriya. Matsalar Najeriya itace amincewa da kuskure da kuma abin da bai dace ba.”

Kara karanta wannan

Ba mu yarda ba: Yarbawa sun ce Tinubu bai ci zabe ba, sun fadi wanda ya lashe zaben bana

Da yake bayyana rashin alakar nasarar Tinubu da tsarin Allah, Obi ya ce, Allah ya hana amfani da sunansa wajen aikin barna.

Sakamakon zabe da yadda Obi ya fusata

A baya idan baku manta ba, an ayyana Bola Ahmad Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Faburairu.

Tinubu ya lallasa ‘yan takarar shugaban kasa 17 a zaben, inda ya fito da kuri’u 8,794,726; kuri’u mafi yawa, wannan ya sa ya lashe zabe kamar yadda dokar kasa ta tanada.

Hakazalika, ya samu kaso 25% na adadin kuri’un da aka kada a jihohi 30, sama da jihohi 24 da kundin tsarin kasa ya bayyana.

Peter Obi da Atiku sun ce za su tafi kotu

Sai dai, Peter Obi da ya zo na uku a zaben, da Atiku da ya zo na biyu a zaben sun bayyana rashin amincewa tare da bayyana maka INEC da Tinubu a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Hukumar INEC ta mamayi Shugaban Kasa, an daga zaben Gwamnoni bai da labari

Gwamna Wike na PDP kuwa, cewa ya yi Obi ne gwarzon zaben bana, domin ya haramtawa ‘yan Arewa ci gaba da mulkin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel