Yadda Wasu Suka Nemi Amfani da Kotu a Karbe Kujerar Abba a Kano Inji Kakakin NNPP
- Oladipupo Olayokun yana da ra’ayin cewa nasarar Abba Kabir Yusuf a kotu za ta agazawa jam’iyyar NNPP
- Sakataren jam’iyyar mai alamar kayan dadi a Najeriya yace an nemi karbe mulkin Kano a damkawa APC
- ‘Dan siyasar ya ce babu dalilin jefa al’umma a cikin dar-dar a shari’ar zaben da aka san NNPP tayi galaba
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Sakataren jam’iyyar NNPP na kasa, Oladipupo Olayokun, ya yi magana da manema labarai a kan siyasar Kano da shari'ar zabe.
A hirar da Punch tayi da shi, Oladipupo Olayokun yace wasu sun nemi yadda za su karbe kujerar gwamna Abba Kabir Yusuf da NNPP a kotu.
A karshe kotun koli ta ba jam’iyyar NNPP nasara, hakan ya kawo karshen takarar Nasiru Gawuna a Kano, abin da ya jefa jama’a a dar-dar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mun godewa bangaren shari’a; mun godewa Ubangiji kuma mun godewa ‘yan Najeriya da al’ummar waje kan abin da ya faru a kotun koli."
"An shiga zabe, muntane sun zabi wadanda suke so. An sanar da sakamako, wanda ya sha kashi ya amince da zaben, ya taya mai nasara murna."
"Sai kurum wadanda suka ji kunya su tafi kotu, bayan an gabatar da hujjoji sai a ga kotu ta saki hanya, aka maimaita kuskuren a kotu na biyu."
- Oladipupo Olayokun
An nemi
Mai magana da yawun bakin na NNPP yace sun ji tsoron wasu za su biyo ta bayan fage domin karbe masu nasarar da suka samu a zaben 2023.
"Babu wani noke-noke, wasu sun so karbe gwamnatin jihar Kano ne ko ta halin ka-ka.
Zabuka biyar aka yi a 2023 a jihohi da Abuja. Zabukan su ne na shugaban kasa, sanatoci, majalisar wakilai, majalisun dokoki da gwamnoni.
Mu dauki misalin Kano. A zabukan, NNPP ta doke APC ciki da waje. ‘Dan takaran shugaban kasan NNPP, Kwankwaso ya doke shugaba Tinubu.
A takarar majalisar wakilai, APC ta samu shida sai NNPP ta samu 18. A majalisar dattawa, NNPP tana da biyu da rinjaye a majalisar dokoki jiha."
- Oladipupo Olayokun
Oladipupo Olayokun yace abin da ya faru kenan a zaben gwamnoni amma sai ga shi APC tana ikirari a kotu cewa Nasiru Gawuna ya ci zabe.
Meya ragewa jam'iyyar Abba da NNPP a kotu?
‘Dan siyasar yace hukuncin da aka yi sun kara farin jinin gwamna Abba Kabir Yusuf ne wanda yace da gwamnatinsa za ta tallata NNPP.
Duk da ake surutun sauya-sheka, daga yanzu zuwa 2027, kakakin jam’iyyar yana sa ran gwamnatin NNPP ta Kano za ta zama abin misali.
Olayokun ya yi farin ciki da aka soke nasarar APC, a cewarsa hakan zai taimaka domin farfado da kimar alkalai da kotu a shari’ar zabe.
An roki Abba da yawo APC?
Rahoto ya zo cewa shugaban APC a Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya roki gwamnan Kano ya bar NNPP bayan hukuncin kotu.
Abdullahi Ganduje yana so Abba Kabir Yusuf da mutanensa su shigo jam’iyyarsu ta APC
Asali: Legit.ng