Jigo a NNPP Ya yi Zancen Yiwuwar Hadewar Abba Da ‘Yan Kwankwasiyya Da Ganduje a APC
- Hadimin gwamnan Kano, Anas Abba Dala, ya sake fitowa ya soki shugaban jam’iyyar APC na kasa
- ‘Dan siyasar yace Abdullahi Umar Ganduje ya kashe APC, hakan ya NNPP damar karbe mulki a 2023
- Dala ya maida martani cewa shugaban na APC ne zai lallabi NNPP da ke gwamnati a jihar Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - A wata hira da aka yi da shi a gidan rediyon Freedom, Anas Abba Dala ya zargi Dr. Abdullahi Umar Ganduje da rusa APC.
Anas Dala shi ne mai taimakawa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf wajen wayar da kan al’umma a game da harkokin siyasa.
Dala: "Ganduje ya kashe APC"
‘Dan siyasar kuma jagora a NNPP mai mulki a yau yace tsohon gwamnan na Kano ya sa son kai wajen tsaida ‘yan takaransu a APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin da Dala yake yi wa Ganduje shi ne ya yi sanadiyyar korar manyan ‘yan jam’iyya domin yaransa ya samu tikiti a 2023.
Umar Abdullahi Ganduje ya yi takarar majalisar tarayya amma ya sha kashi a hannun Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe na NNPP.
Anas Dala ya shaidawa tashar rediyon cewa Gandujiyya ta zalunci Abdulrahman Kawu Sumaila, ta hana shi yin takara a APC.
Mai ba gwamna Abba shawara ya yi ikirarin Kawu Sumaila ya samu takarar Sanata da ‘dan majalisa amma aka hana shi tsayawa.
Shigowar Abdullahi Ganduje Kano
An yi hira da ‘dan siyasar ne ganin Abdullahi Ganduje zai ziyarci Kano a karon farko tun da ya bar kan gadon mulki a Mayun 2023.
Dala yace babu zai hana tsohon gwamnan shigowa Kano, asali ma suna son ganinsa domin mutane su gane irin nauyinsa a siyasa.
Hadimin gwamnan yace jama’a za su kamanta zuwansa da tarbar da aka yi wa gwamna Abba bayan nasararsa a kotun koli.
Abba zai koma APC a Kano?
A kan rokon sauya-sheka zuwa APC, Dala yace Ganduje ne zai zo zawarcin ‘yan NNPP ba su za su tafi wajen shugaban jam’iyya ba.
‘Dan siyasar yace Bola Tinubu ya bada umarni a jawo NNPP mai mulki domin kuwa yawan mutane shi ne kasuwa ba tarin rumbuna ba.
Sai an kori mutane a APC ta Kano
Kwanan aka samu labari jagoran Win-Win, Muazu Magaji ya bukaci a kori wasu shugabannin jam’iyyar APC 3 a reshen jihar Kano.
Magaji yace wadannan mutane su ne dai suka kayar da APC a 2019 da kuma 2023, don haka dole ne a fatattake su domin ayi gyara.
Asali: Legit.ng