An Yaudari Mutane a 2023 da Tikitin Musulmi da Musulmi Inji Tsohon Mutumin Buhari

An Yaudari Mutane a 2023 da Tikitin Musulmi da Musulmi Inji Tsohon Mutumin Buhari

  • Buba Galadima yana ganin yaudarar al’umma aka yi da addini a tikitin Bola Tinubu/Kashim Shettima
  • ‘Dan siyasar ya ce bai dace talaka ya rudu da karyar addinin ‘yan siyasa ba, akwai yaudara a lamarinsu
  • Fitaccen ‘dan siyasar ya fadawa Legit Hausa malaman addini su rike fagen wa’azinsu su daina shiga harkarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Buba Galadima da jam’iyyarsa ta NNPP mai alamar kayan marmari sun sa kashi a zaben shugaban kasa da aka yi a 2023.

Buba Galadima ya yi magana da Legit Hausa a ranar Litinin, inda ya yi tsokaci game da siyasar Najeriya da abin da ya faru a zaben bara.

Buba Galadima
Buba Galadima a kan tikitin APC Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

An ci da addini a zaben 2023?

Jigon na jam’iyyar NNPP yana ganin an dauki darasi a zaben 2023 domin a ra’ayinsa, ‘yan siyasa sun shiga rigar addini sun samu mulki.

Kara karanta wannan

Mai ba Jonathan shawara ya nunawa Tinubu hanyar farfado darajar Naira kan Dala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam’iyyar APC ta tsaida tikitin musulmi da musulmi, masu fashin baki suna ganin wannnan ya taimaki Bola Tinubu da Kashim Shettima.

Malaman addinin musulunci da-dama sun tallata tikitin Bola Tinubu/Kashim Shettima a yau kuma wasunsu suna kuka da gwamnati.

Buba Galadima a kan malamai da tikitin musulmai

‘Dan siyasar ya fadawa Legit Hausa bai kamata mutane su rudu da tikitin musulmi-musulmi ba domin ‘dan siyasa ya fi kowa sanin ‘yan siyasa.

Galadima ya nanata shawarar cewa malaman addini su tsaya a matsayinsu, a bar ‘yan siyasa a fagen su, sai kowa ya rike huruminsa.

Abin da Buba Galadima ya fadawa Legit Hausa

“Mu ne muka san junanmu ‘yan siyasar nan, mun san na-kirki, bara-gurbi, mutumin banza da kuma manufuki"
"Mun san azzalumi wanda zai iya yin komai domin bukatar kan shi. Mun san juna tare muke sallah ko zuwa coci."

Kara karanta wannan

EFCC ta gano kungiyar addini da ke taimakon ‘yan ta’adda

"Mu ne muka san wanda addininsa na karya ne! yanzu dai ‘yan Musulmi da musulmi me suka samu (a mulkin APC)"

- Buba Galadima

Me tikitin APC ya tsinana a yau?

Injiniya Buba Galadima yace a ‘yan siyasa akwai mutanen kwarai da akasinsu, kuma sai wadanda suka zauna da su ne za su fahimta.

Tsohon jagoran na APC mai mulkin Najeriya yake cewa kusan kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, musulman da suka yi zabe suna kuka.

Tinubu: Buba Galadima ya san za a rina

Watanni kadan da hawa mulkin Bola Tinubu sai ga shi ana kukan za a dauke wasu ofisoshin daga babban birnin tarayya zuwa jihar Legas.

Buba Galadima yace tun a lokacin yakin neman zabe ya haskawa al’umma hakan za ta faru, amma hakan bai hana a zabi jam’iyyar APC ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng