Buhari Ya Faɗi Dalilin da Ya Sa Gwamnatinsa Ba Ta Kashe Wani Shugaban Ƴan Ta'adda Ba, Ta Masa Gata 1

Buhari Ya Faɗi Dalilin da Ya Sa Gwamnatinsa Ba Ta Kashe Wani Shugaban Ƴan Ta'adda Ba, Ta Masa Gata 1

  • Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce gata gwamnatinsa ta yi wa shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB
  • A littafin da tsohon kakakin Buhari, Femi Adesina ya rubuta, Buhari ya faɗi yadda gwamnatinsa ta taso ƙeyar Kanu zuwa Najeriya
  • Adesina ya bada labarin yadda ta wakana yayin da wasu manyan Ibo suka roki tsohon shugaban ƙasar ya sa baki a saki Kanu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon mai baiwa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya ce gwamnatin Buhari gata ta yi wa Nnamdi Kanu.

Ya bayyana cewa taso ƙeyar shugaban haramtacciyar kungiyar ƴan aware (IPOB), Kanu, zuwa Najeriya daga inda ya ɓuya gata ne gare shi, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kano: Kwankwaso Ya faɗi makircin da aka Shirya ƙulla masa idan Gawuna ya yi nasara a Kotun Koli

Nnamdi Kanu da Buhari.
Da Mun So Zamu Kawar da Nnamdi Kanu a Can Inda Ya Buya, Buhari Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Adesina ya bayyana hakan ne a cikin littafinsa mai suna ‘Reflections of a Special Adviser, Media and Publicity (2015-2023), wanda aka kaddamar a Abuja a makon jiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan baku manta ba a watan Yuni, 2021 aka taso ƙeyar Kanu zuwa Najeriya bayan ya sa ƙafa ya shure sharuɗɗan belin da babbar kotun tarayya ta ba shi, The Cable ta tattaro.

Kotun ta bada belin shugaban IPOB ne bayan gurfanar da shi a gabanta kan tuhume-tuhume 11 da suka kunshi cin amanar kasa, ta'addanci da dai sauransu.

Buhari ya faɗi gatan da ya yi wa Nnamdi Kanu

Yayin da wata tawaga ƙarƙashin manyan ƙabilar Igbo ta kai wa tsohon shugaban ziyara don ya saki Kanu, Adesina ya haƙaito Buhari na ba su amsa da cewa:

"A shekaru shida da suka wuce, na kafa tsarin da ni dai ba zan tsoma baki a harkokin shari'a ba, shiyasa kes ɗin Kanu, na ce abin da ya fi dacewa a miƙa wa shari'a ta yi aikinta."

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan CBN ya faɗi gaskiyarsa kan tuhume-tuhume 20 da ake masa a gaban kotu

"A bari ya kare kansa a gaban kotu kan mummunan ra'ayin da yake yaɗawa a kasar nan. Ni ina ganin gata muka masa da muka ba shi wannan damar. Idan gwamnati ta so zata iya kitsa yadda za a kashe shi a inda ya buya amma ba mu yi haka ba."
"Kun bukaci abu mai wahala daga wuri na a matsayin na jagoran ƙasar nan, batu ne mai girma, na san a shekara 6 da ta wuce, ba wanda zai yi tunanin zan yi katsalandan a shari'a, amma zan duba."

Wani abu ya fashe a Kaduna

A wani labarin kun ji cewa Rahotanni sun bayyana cewa wani abu da ake zargin 'Bam' ne ya tashi a garin Kidandan, ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa a bayanan da ta samu daga jami'an tsaro, mutum ɗaya ya mutu yayin da wasu 10 suka ji rauni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel