Soyinka: An Yi Makarkashiyar Hana Zabe ko a ki Rantsar da Tinubu Irin na Shekarar 1993
- Farfesa Wole Soyinka ya yi ikirarin akwai yunkurin da aka yi domin a hana zaben Najeriya ya tabbata
- Marubucin ya ce ko da an yi zaben, an nemi hana hukumar INEC tabbatar da wanda ya samu galaba
- Farfesa Soyinka yana da ra’ayin cewa saura kiris a maimaita abin da aka yi a lokacin zaben 1993
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Fitaccen marubucin duniyan nan, Wole Soyinka, ya ce wasu sun yi kutun-kutun domin soke zaben da aka yi a 2023.
Farfesa Wole Soyinka ya shaidawa tashar Channels cewa an nemi rusa zaben da Bola Ahmed Tinubu ya lashe a shekarar bara.
An kusa maimaita 1993 a zaben 2023 inji Soyinka
Wole Soyinka ya yi ikirarin saura kiris tarihi ya maimaita kan shi kamar yadda aka gani a mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A lokacin Ibrahim Badamasi Babangida ne aka shirya zabe kuma saura kiris MKO Abiola ya samu nasara, sai sojoji suka rusa zaben.
"Saura kiris tarihi ya maimaita kan shi, wasu mutane sun dage sai sun maida mu zamanin da."
"Ina zargin an shirya makarkashiya tun farko kafin zaben domin a tabbatar da cewa ba ayi zaben ba"
"Ko kuwa ko da mutane sun kada kuri’a, sai a ruguza kamar yadda ta faru a mulkin Janar Babangida"
- Wole Soyinka
Wole Soyinka a kan zaben 1993
Soyinka ya shaidawa gidan talabijin yadda ta faru a zaben 1993, yake cewa an farka daga barci kurum aka ji gwamnati ta rusa zaben.
Farfesan ya ce takarar ba tsakanin ‘yan siyasa ba ce, ana neman ceto damukaradiyya ne, saboda haka ya san wanda ya dace ya goyi baya.
Ba wannan ne karon farko da aka ji Soyinka ya soki gwamnatin Muhammadu Buhari ba.
Soyinka ya sake caccakar Datti Baba-Ahmed
Punch ta ce Soyinka ya sake yin kaca-kaca da Datti Baba-Ahmed a kan hirar da aka yi shi bayan LP ta sha kashi a hannun Bola Tinubu.
Marubucin ya ce abokin takarar na Peter Obi ya yi abin kunya wajen sukar tsarin da ya taimaka masa wajen zama gwamna a Najeriya.
Hasashen zaben 2027
Ana da labari Reno Omokri ya ce idan Peter Obi bai tsaya takara a 2027 ba, Atiku Abubakar zai iya doke Bola Tinubu da APC mai-ci.
Idan ba haka ba kuwa, jagoran na PDP ya ce za a maimaita sakamakon zaben 2023 inda Obi ya raba kuri'un magoya bayan 'yan adawa.
Asali: Legit.ng