Yaki da rashin gaskiya: Shugaban kasa Buhari ya sallama inji Wole Soyinka
- Farfesa Wole Soyinka ya ce gwamnatin APC ta sare a yaki da rashin gaskiya
- Wole Soyinka ya ce da ace gwamnati ba ta sare ba, da an daure barayin kasa
- Kwanakin baya, Farfesan ya ce bai son yin magana a kan gwamnatin Buhari
Shahararren Farfesan nan, Wole Soyinka, ya sake yin magana game da gwamnatin Muhammadu Buhari, bayan a da ya ce bai jin dadin magana a kanta.
Farfesa Wole Soyinka ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta sare a yakin da ta daukar wa kanta alkawari na kawo karshen rashin gaskiya a Najeriya.
A cewarsa, wannan ya jawo wasu kusoshi da ke da karfi a gwamnati su na wasa da hankalin kotu.
Punch ta rahoto Farfesan ya na wannan bayani a ranar Laraba, 27 ga watan Junairu, 2021, lokacin da aka yi hira da shi a shirin Kakaaki a gidan talabijin na AIT.
KU KARANTA: Ba Buhari ya ke sarrafa sha'anin mulkin kasar nan ba - Wole Soyinka
Fitaccen marubucin ya ce tsarin shari’ar da ake kai a kasar ya gurbace matuka ta yadda ake bata lokaci fiye da kima wajen shari’a a kotu saboda wasu ka’idoji.
“Akwai mutane da yawa da ya kamata ace suna gidan yari, idan da gwamnatin nan ba ta gaji ba. Saboda haka, ana wasa da tsarin shari’a.” inji Farfesa Soyinka.
“Akwai shari’o’in da masu kara sun kai matakin gabatar da hujjojin da ke nuna satar gwamnoni a gaban kotu” Ya ce kwatsam kuma sai aji maganar ta koma ta yi tsit.
Wole Soyinka ya yaba da irin kokarin da EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin Najeriya zagon-kasa, ta yi a lokaci da Nuhu Ribadu ya ke jagorantar hukumar.
KU KARANTA: Najeriya mota ce maras direba inji Wole Soyinka
Da yake magana game da kira da ake yi na canza wa tsarin shugabanci kasa fasali, masanin ya ce abin da ya dace shi ne ‘yan majalisa su daina biyewa gwamnati.
Kwanakin baya da aka yi masa tambaya, Darfesa Wole Soyinka ya ce bai son yin magana kan gwamnati mai-ci da Shugaba Muhammadu Buhari ya ke jagoranta.
Fitaccen marubucin ya ce idan har mutum bai son ya 'zautu' ya fi alheri ya kauda hankalinsa.
Amma duk da hakan, ko a lokacin Wole Soyinka ya ce ya yi farin cikin ganin yadda gwamnatin tarayya ta gyara layukan dogo da kuma kawo sababbin jiragen kasa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng