Bayan shekaru kusan 30, Obasanjo ya bayyana dalilin Sojoji na kashe zaben MKO Abiola

Bayan shekaru kusan 30, Obasanjo ya bayyana dalilin Sojoji na kashe zaben MKO Abiola

- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya yi magana game da zaben 1993

- Olusegun Obasanjo ya ce ‘bukulu’ ne ya hana MKO Abiola zama Shugaban kasa

- Obasanjo ya bayyana wannan ne a lokacin da Abeokuta Club ta karrama su jiya

A ranar Lahadi, 11 ga watan Afrilu, 2021, tsohon shugaban kasa, Janar Olusegun Obasanjo mai ritaya ya tabo maganar zaben da aka yi a shekarar 1992.

Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatin sojan wancan lokaci ta soke zaben shugaban kasar da aka yi ranar 12 ga watan Yunin 1993.

A cewar tsohon shugaban Najeriyar, an kashe zaben da ake kyautata zaton Marigayi Moshood Kashimawo ‘MKO’ Abiola ya lashe ne saboda ‘bakin-ciki’.

KU KARANTA: Takaitaccen tarihin Janar Ibrahim Badamasi Babangida

Jaridar Daily Trust ta ce Olusegun Obasanjo ya yi wannan bayani ne yayin da ya hadu da ‘yan kungiyar mutanen Egba watau Abeokuta Club a jihar Ogun.

Obasanjo ya nuna takaicinsa a game da soke wannan zaben shugaban kasar da aka yi, ya ce wannan mataki da aka dauka ya na da tasiri kan yankin Aboekuta.

A wajen wannan taro, an nada Marigayi MKO Abiola a matsayin daya daga cikin shugabannin kungiyar nan ta Abeokuta Club ta kabilar Yarbawan Egba.

MKO Abiola abokin karatun tsohon shugaban kasa Obasanjo ne, wanda ya bayyana cewa Marigayin ya cancanci karrama war da kungiyar ta yi masa.

KU KARANTA: Obasanjo na da hannu wajen soke zaben 1993: - Babagana Kingigbe

Bayan shekaru kusan 30, Obasanjo ya bayyana dalilin Sojoji na kashe zaben MKO Abiola
Obasanjo ya ce 'yan bakin-ciki su ka hana MKO Abiola mulki
Asali: Twitter

Da ace an bar wannan zabe wanda Moshood Abiola ya kai daf da samun nasara, da Yarbawan Egba uku su ka rike kujerar shugaban kasa a Najeriya inji Obasanjo.

Bayan Obasanjo wanda ya fito daga cikin Yarbawan Egba da Marigayi Abiola wanda aka yi wa bukulu, an samu Ernest Shonekan wanda ya yi mulkin Najeriya.

A wajen wannan taro, Alake wanda shi ne babban Sarkin kasar Egba, Oba Adedotun Aremu Gbadebo ya ba Obasanjo lambar yabo a matsayinsa na abin alfaharinsu.

A bara ne aka ji cewa Dakarun ‘yan sandan jihar Legas sun tsare wasu ‘ya ‘ya biyu daga cikin iyalin marigayi Moshood Kasimawo Olawale Abiola da laifin sata.

Jami’an tsaron sun tsare ‘ya ‘yan marigayin da kuma wasu ma’aikatan gidansa uku bisa zarginsu da ake yi da laifin hannu a fashin da aka yi a gidan tsohon Attajirin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel