Uba Sani da Sauran Cikakken Jerin Gwamnonin da Kotun Koli Za Ta Yanke Hukunci Kan Nasararsu

Uba Sani da Sauran Cikakken Jerin Gwamnonin da Kotun Koli Za Ta Yanke Hukunci Kan Nasararsu

FCT, Abuja - Ƙararraki da dama sun biyo bayan zaɓen da hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta gudanar na gwamnoni a shekarar 2023.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ya zuwa ranar Asabar 13 ga Janairu, 2024, gwamnoni 10 ne suka yi nasara a Kotun Ƙoli.

Gwamnonin da Kotun Koli ba ta yi hukunci a shari'ar zabensu ba
Akwai akalla gwamnoni takwas dake jiran sanin makomarsu a Kotun Koli Hoto: Abdullahi Sule, Sir Siminalayi Fubara, Senator Uba Sani
Asali: Facebook

A cewar shugabar kotun ɗaukaka ƙara, Mai shari’a Monica Dongban-Mensem, ƴan takarar gwamna a jihohin Kwara, Neja,Yobe da Katsina ba su ƙalubalanci sakamakon zaɓen a kotu ba.

Kotun Ƙoli ba ta yanke hukunci kan ɗaukaka ƙara daga jihohin Rivers, Kaduna, Nasarawa, Sokoto, Gombe, Kebbi da Taraba da dai sauransu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan yana nufin za a yanke hukunci kan makomar aƙalla gwamnoni 8 a Kotun Ƙoli, wacce ita ce mai yanke hukunci na karshe.

Kara karanta wannan

Kotun koli ta tanadi hukunci kan sahihancin nasarar gwamnan arewa, APC na tsaka mai wuya

Ga gwamnonin da Kotun Ƙoli ba ta yanke hukunci kan makomarsu ba:

1) Siminalayi Fubara (Jihar Rivers)

Kotun Ƙoli a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu, ta tanadi hukunci a ƙarar da ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Tonye Cole, ya shigar kan nasarar da Gwamna Siminalayi Fubara ya samu a zaɓen gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, 2023

Kotun mai alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta tanadi hukunci kan ɗaukaka ƙarar bayan dukkan bangarorin da ke ƙarar sun kammala bayanansu.

2) Abdullahi Sule (Jihar Nasarawa)

Kotun Ƙoli ta tanadi hukunci kan ƙarar da jam’iyyar PDP da ɗan takararta David Ombugadu suka shigar inda suke ƙalubalantar nasarar Abdullahi Sule na jam’iyyar APC a matsayin gwamnan jihar Nasarawa.

A ranar Talata, 16 ga watan Janairu, kotun mai alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Kekere-Ekun ta tanadi bayan lauyoyin masu lara da wadanda ake ƙara sun kammala bayanansu na ƙarshe.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya shirya liyafa bayan nasara a kotun koli, ya aike da muhimmin saƙo ga Bola Tinubu

3) Ahmad Aliyu Sokoto (Jihar Sokoto)

A watan Nuwamba 2023, Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta tabbatar da Ahmad Aliyu na jam’iyyar APC a matsayin gwamnan jihar Sokoto.

Tun da farko, a watan Satumba, kotun zaɓe ta kuma tabbatar da zaɓen Gwamna Aliyu.

4) Muhammad Inuwa Yahaya (Jihar Gombe)

A watan Nuwamba 2023, kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da zaɓen gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya.

Da yake karanta hukuncin, mai shari’a T. N Orji-Abadua ya tabbatar da nasarar gwamnan tare da yin watsi da ƙarar da jam’iyyar PDP da ɗan takararta, Jibrin Barde suka shigar.

5) Nasir Idris (Jihar Kebbi)

Kotun Ƙoli a ranar Talata, 16 ga watan Janairu, ta tanadi hukunci kan taƙaddamar zaɓen gwamna tsakanin Gwamna Nasir Idris na APC da Aminu Bande na PDP.

Kotun mai alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Kekere-Ekun ta tanadi hukuncin ne bayan ɓangarorin da suka shigar da kara sun kammala gabatar da bayanansu.

Kara karanta wannan

Jigon NNPP ya fadi abu 1 da zai faru da alkalan Kotun Koli da Gwamna Abba ya yi rashin nasara

6) Agbu Kefas (Jihar Taraba)

Kotun ɗaukaka ƙara a watan Nuwamba 2023 ta tabbatar da zaɓen Kefas Agbu a matsayin gwamnan jihar Taraba.

A wani hukunci na bai daya da alƙalan kotun mai mutum uku da mai shari’a Peter Afen ya yanke, kotun ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar NNPP da ɗan takararta na gwamna, Farfesa Yahaya Sani.

7) Sanata Uba Sani (Jihar Kaduna)

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja a watan Nuwamba 2023 ta tabbatar da zaɓen Uba Sani a matsayin gwamnan jihar Kaduna.

A halin da ake ciki, Kotun Ƙoli ta tanadi hukunci kan ƙarar da PDP da ɗan takararta Isah Ashiru suka ɗaukaka, kan nasarar Gwamna Uba Sani.

8) Sheriff Oborevwori (Jihar Delta)

A farkon watan Janairu ne Kotun Ƙoli ta tanadi hukunci kan ƙarar da jam’iyyun APC, SDP da LP ƴan takararsu suka yi a zaɓen gwamnan jihar Delta na shekarar 2023.

Kotun Ƙoli mai alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin John Okoro bayan sauraron muhawarar jam’iyyun ta tanadi hukunci kan batutuwan.

Kara karanta wannan

Kotun koli ta yanke hukuncin ƙarshe kan ƙarar da aka nemi tsige gwamnan PDP daga mulki

Gwamnonin da Kotun Ƙoli Ta Sauya Korarsu

A baya rahoto ya zo kan gwamnonin da Kotun Ƙoli ta sauya korar da aka yi musu a kotun ɗaukaka ƙara.

Gwamnonin Kano da Plateau na daga cikin waɗanda Kotun Ƙoli ta sauya hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yi na korarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng