Yadda APC Ta Ci Banza da Kotu Tayi Kuskuren Tsige ‘Yan Majalisa da Sanatocin PDP 22

Yadda APC Ta Ci Banza da Kotu Tayi Kuskuren Tsige ‘Yan Majalisa da Sanatocin PDP 22

  • Nasarar Caleb Mutfwang a kotun koli ya tabbatar da kuskuren alkalan kotun daukaka kara a shari’ar Filato
  • Alkalan Kotun koli sun ce babu wanda yake da hurumin soke takarar ‘yan PDP saboda kin yi wa kotu biyayya
  • Babban kotun ta ci gyaran hukuncin da ya ci ‘yan majalisan jam’iyyar PDP a Filato da aka tsige daga kan mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Plateau - Kotun daukaka kara ta tsige gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang da duka ‘yan majalisan da aka zaba a karkashin PDP a bara.

Amma da aka je kotun koli, sai ga shi alkalai sun dawo da Mai girma Caleb Mutfwang a mulki, aka rusa hukucin da aka yi a baya.

Kara karanta wannan

Kano: Sanusi II ya soki APC a maganar farko a fili bayan nasarar Abba a Kotun Koli

Majalisa da Sanatocin PDP
Wasu 'yan majalisa a bakin aiki Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

John Inyang Okoro ya ce alkalai sun yi kuskure wajen tsige wadanda aka zaba a PDP bisa zargi rashin hurumin tsaida ‘yan takara a 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC a Filato: Ruwa ta sha a zaben 2023?

Amma da yake an kammala shari’ar ‘yan majalisar dokoki da ‘yan majalisar tarayya, ba su da damar cin moriyar hukuncin a halin yanzu.

Mai shari’a John Inyang Okoro ya koka a kan yadda PDP ta rasa sanatoci biyu, ‘yan majalisar wakilai 5 da ‘yan majalisa har 16 na jihohi.

A sakamakon shari’ar nan ne Simon Lalong ya zama sanata, kotun daukaka kara ta mika kujera ga wasu ‘yan takara 22 da PDP ta doke.

Hukuncin kotun kolin ya hana Nentawe Yilwatda da APC karbe mulkin jihar Filato. Hakan ya jawo suka ga Monica Dongban-Mensem.

Ba a shari'ar majalisa a kotun koli

Kara karanta wannan

Batun sace 'yan matan Abuja: Peter Obi ya koka kan yadda 'yan Najeriya suka rasa 'yanci

A dokar Najeriya, shari’ar ‘yan majalisa ba ta zuwa kotun koli, karar zaben gwamnoni da na shugaban kasa kadai ake yi a kotu har uku.

Premium Times ta ce saboda haka ne lauyoyi suka fara bada shawarar a canza doka ta yadda ‘yan majalisa za su iya daukaka shari’ar.

Wadanda aka kora a majalisa da kuskure

Irinsu Dachung Bagos, Peter Gyendeng, Musa Agah, Beni Lar da Isaac Kwalu sun rasa kujerunsu duk da kotu tayi kuskure a hukuncinta.

A sanadiyyar haka Dalyop Chollom, Ajang Iliya, Venman da kuma Muhammad Alkali da John Dafa’an su ka samu kujerun majalisa a sama.

Shari'ar Kano a kotun koli

An ji labarin yadda John Okoro ya yi amfani da doka da ilmin shari’a, ya warware hukuncin kotun korafin zabe da daukaka kara a Kano.

A.B. Mahmoud SAN ya kare Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da halaccin kuri’un NNPP inda Oluwole Olanipekun, SAN, OFR ya doke APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng