Takaitaccen tarihin rayuwar Jastis Mensem, sabuwar shugabar kotun daukaka kara

Takaitaccen tarihin rayuwar Jastis Mensem, sabuwar shugabar kotun daukaka kara

A ranar Alhamis ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da zabin Jastis Monica Bolna'an Dongban-Mensem a matsayin sabuwar shugabar kotunan daukaka kara na Najeriya.

Jastis Mensem, mai shekaru 62 a duniya, ta maye gurbin tsohuwar shugabar kotunan daukaka kara, Jastis Zainab Bulkachuwa, wacce ta yi ritaya daga aiki a wannan watan.

Babbar alkaliyar, 'yar asalin jihar Filato, ta shiga bakin manema labarai bayan an ganta sanye da kaki tana sarrafa cunkuson ababen hawa a birnin tarayya (FCT), Abuja.

Wani iftila'i ya taba fada wa a kanta shekaru takwas da suka gabata, yayin da yaronta ya mutu a hatsarin mota. Tun daga lokacin da kulla damarar tabbatar da kiyaye afkuwar tsari a tituna.

Jastis Mensem ta fara aiki ne da ma'aikatar shari'a ta jihar Filato a shekarar 1979 bayan ta kammala karatun digir na farko (LL. B) da na biyu (LL.M) a bangaren shari'a daga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Takaitaccen tarihin rayuwar Jastis Mensem, sabuwar shugabar kotun daukaka kara

Jastis Mensem
Source: UGC

Ta yi aiki a wurare da dama a matsayin alkaliyar kotun majistare da kuma babbar alkaliyar kotun majistare a tsakanin 1981 zuwa 1990.

DUBA WANNAN: Sarki Sanusi II: Al'ummar unguwar Ja'en sun nesanta kansu daga takardar korafi, zasu yi karar majalisa

Jastis Mensem ta zama alkaliya a hukumar shari'a ta birnin tarayya (FCT) daga shekarar 1997 zuwa 2003

Ta na yin abubuwa da yawa; alal misali, ta dauki nauyin wani shiri da ake yi kullum a gidan radiyon 'Tin City FM' domin bawa kananan yara labarai masu dadi cikin littafin 'Injila'.

Ta taba rike mukamin mukaddashin shugabar kotunan daukaka kara da ke jihar Legas daga watan Nuwamba zuwa Disamba na shekarar 2009.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel