Yadda Tinubu Ya Warware Abin da Ganduje Ya So a Shiryawa Kano a Kotun Koli Inji Abba

Yadda Tinubu Ya Warware Abin da Ganduje Ya So a Shiryawa Kano a Kotun Koli Inji Abba

  • Abba Kabir Yusuf ya zargi magabancinsa da neman amfani da matsayinsa wajen canza hukuncin kotun koli
  • Gwamna Abba ya ce Abdullahi Umar Ganduje ya yi yunkurin ganin an tursasa alkalai a kan zaben jihar Kano
  • Dr. Ganduje wanda shi ne shugaban APC bai maida martani a kan wannan babban zargi da ake jifansa da shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta jinjinawa shugaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa watau Sanata Kashim Shettima.

Godiyar ta zama dole ne bayan nasarar da jam’iyyar NNPP ta samu a kotun koli a kan shari’ar zaben gwamnan Kano da aka yi a 2023.

Abdullahi Ganduje
Abdullahi Ganduje tare da Shugaban kasa Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

A wani jawabi da ya fito ta bakin Sanusi Bature Dawakin-Tofa, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce an yi yunkurin canza hukuncin kotu.

Kara karanta wannan

Mutane 6 da Suka Taimakawa Abba Kabir Yusuf Wajen Samun Nasarar Kotun Koli

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya so APC tayi nasara a kotun koli

Darekta Janar na yada labaran ya ce Abdullahi Ganduje ya hurowa shugaban kasa wuta wajen ganin alkalan kotu sun ba APC nasara.

Mai magana da yawun gwamnan Kano ya ce watsi da bukatar Abdullahi Ganduje ya nuna Najeriya tayi dace da shugabanni a halin yanzu.

Punch ta ce an nemi jin ta bakin shugaban jam’iyyar APC na kasa watau Abdullahi Ganduje a kan wannan zargi, amma ba a dace ba.

Kotun koli: An ci amanar 'yan APC a Kano

Salihu Tanko Yakasai ya yi magana a Facebook, ya nuna faduwa zabe ko rashin nasara a kotu bai yi masu ciwo ba kamar cin amana ba.

Hadimin shugaban na APC ya zargi wasu da juya-masu baya, amma bai kama suna ba.

"Wato faduwa ba ita ce matsala a siyasa ba, dama kowa ya san akwai nasara akwai akasin ta. Amma kaga cin amana daga wanda ka ba amana? Itace ciwon!"

Kara karanta wannan

Kano: Sanusi II ya soki APC a maganar farko a fili bayan nasarar Abba a Kotun Koli

- Salihu T. Yakasai

Sakataren yada labaran APC na Kano, Ahmed Aruwa ya ce ba zai iya cewa uffan a kan lamarin ba har sun zauna da shugaban jam’iyya na kasa.

..."an hana mu magana" - Hadimin Ganduje

Aminu Dahiru Ahmad da yake tofa albarkacin bakinsa, ya ce akwai tulin maganganu a bakinsu amma jagororinsu a APC sun hana su yin magana.

Malam Aminu Ahmed yana aiki da Ganduje a matsayin mai taimakawa wajen sadarwa.

Wata majiya ta ce Ganduje ya nemi zama da Bola Tinubu ranar Alhamis, amma hakan bai yiwu ba, a ranar hukuncin ya yi taro da gwamnoni.

A karshe ana da labari kotun koli ta soke nasarorin da aka ba Nasiru Gawuna, ta ce NNPP ta lashe zabe, hukuncin da bai yi wa APC mai-ci dadi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng