Jerin Gwamnonin Da Kotun Koli Ta Sauya Korar Da Kotun Daukaka Kara Ta Yi Musu
A ranar Juma’a 12 ga watan Janairu ne Kotun Ƙoli ta saurari ƙararrakin zaɓen gwamnoni da bai gaza takwas ba, kotun ɗaukaka ƙara ta kori wasu daga cikinsu a baya.
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Sai dai gwamnonin da aka kora sun samu nasara a Kotun Ƙoli a ranar Juma’a, kuma za su ci gaba da riƙe kujerunsu har zuwa zaɓe mai zuwa.
Ga jerinsu a nan ƙasa:
Gwamna Abba Kabir Yusuf
Kotun Ƙoli ta soke korar gwamnan jihar Kano da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kano da kotun ɗaukaka ƙara ta tuɓe a baya, cewar rahoton Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun Ƙolin dai ta nuna kuskuren cire ƙuri’un gwamnan da aka yi, inda ta ce ƙuri’un da ba a ba jami’an zaɓe ba ne kawai za a ce ba su da inganci.
Ta yanke hukuncin cewa batun zamansa ɗan jam'iyya batu ne na cikin gida ne wanda bai shafi wasu daban ba.
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kano ta kori Gwamna Yusuf bayan cire wasu ƙuri’un da ya samu waɗanda ta ce ba su da inganci.
A kotun ɗaukaka ƙara, an tsige gwamnan ne bisa dalilin cewa shi ba ɗan jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ba ne.
Gwamna Caleb Mutfwang
Kamar dai saura, a ranar Juma’a, 12 ga watan Janairu, Kotun Ƙolin ta yanke hukunci kan ƙarar da aka shigar na neman sauya korar Gwamna Mutfwang na jihar Plateau, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.
Kotun ta yi watsi da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke tun farko da ta kori gwamnan tare da tabbatar da nasarar ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamnan da aka yi ranar 18 ga watan Maris.
Kamar yadda ta yanke hukunci kan makomar Gwamna Yusuf na Kano kan batun takara, Kotun Ƙolin ta tsaya tsayin daka kan cewa batun takara abu ne na cikin gida.
Dauda Lawal
Kotun Ƙoli ta tabbatar da zaɓen Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara, wanda kotun ɗaukaka ƙara ta kora tun da farko.
Mai shari’a Emmanuel Agim, wanda ya yanke hukuncin, ya bayyana hukuncin kotun ɗaukaka ƙara a matsayin karkatacce.
Kotun Ƙolin ta ce:
"Hukuncin da Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke ba shi da hujja mai tushe."
Jigon NNPP Ya Yi Magana Kan Shari'ar Gwamnan Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar NNPP ya yi magana kan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan shari'ar zaɓen gwamnan Kano.
Ibrahim Danlami Kubau ya bayyana cewa hukuncin babbar nasara ce ga dimokuraɗiyyar Najeriya da ƴan Najeriya.
Asali: Legit.ng