Kwankwaso Ya Fasa Kwai, Ya Ce ‘Gawuna Bai Ci Zaben Kano ba, ko a 2019 Murdiya Aka Yi’

Kwankwaso Ya Fasa Kwai, Ya Ce ‘Gawuna Bai Ci Zaben Kano ba, ko a 2019 Murdiya Aka Yi’

  • Nasiru Yusuf Gawuna ya san Abba Kabir Yusuf ya doke shi a zaben Kano a 2023 a cewar Rabiu Musa Kwankwaso
  • Tsohon Gwamnan Jihar Kano ya ce a karshe jagororin APC irinsu Abdullahi Umar Ganduje sun rasa darajarsu
  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yake cewa da farko Nasiru Gawuna ya rungumi kaddara, bai shirya zuwa kotu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Rabiu Musa Kwankwaso ya yi ikirarin ‘dan takaran APC, Nasiru Yusuf Gawuna bai ci zaben gwamnan jihar Kano ba.

Tsohon Gwamnan na jihar Kano ya bayyan wannan ne a wata zantawa da ya yi da TRT Hausa bayan nasarar NNPP a kotun koli.

Kwankwaso
Gawuna, Kwankwaso da Ganduje Hoto: @SaifullahiHon, @Dawisu
Asali: Twitter

Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi Nasiru Yusuf Gawuna da neman mulki a sama, yake cewa a tunaninsa zai samu ne a bati.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana kan shiga gwamnatin Tinubu da APC mai mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rabiu Kwankwaso ya caccaki Ganduje

Jagoran na NNPP mai mulkin Kano ya caccaki Abdullahi Umar Ganduje da aka nemi ya aika sako ga shugaban jam'iyyar APC na kasa.

Tsohon gwamnan yake cewa magajinsa a Kano ya zubar da darajarsa a siyasa kuma ba zai fahimci hakan ba sai nan gaba kadan.

"Shi ma Gawuna ya yi asara" - Kwankwaso

Kwankwaso ya shaidawa gidan rediyon cewa haka zalika Nasiru Gawuna ya yi babban asara wajen neman zama gwamnan Kano.

‘Dan siyasar yake cewa mutunci kamar madara ne, idan aka yi barinsa to ba za a dauke ba, yana shagube ga tsohon gwamnan jihar.

Jaridar Aminiya ta ce a hirar da aka yi da shi, ‘dan takaran shugaban kasar a zaben 2023 ya ce bai kamata mutum ya rasa darajarsa ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya bayyana babban abin da ya ke mutunta Tinubu da shi bayan hukuncin Kotun Koli

Kwankwaso ya ce duk abin da za ayi da sunan siyasa da neman takara, bai dace ayi asarar mutunci kamar yadda wasu suka yi ba.

Me ya kai Nasiru Gawuna kotu?

Babban ‘dan siyasar ya kara da cewa da farko Nasiru Gawuna ya gamsu ya fadi takara, daga baya aka zuga shi ya garzaya kotun zabe.

Kwankwaso ya ce an nunawa ‘dan takaran na APC zai iya cin banza kamar yadda aka yi a 2019. Sai dai jam'iyya ce ta shigar da kara a kotu.

A cewar Kwankwaso, jama’a sun rika addu’o’i dare da rana saboda nasarar NNPP, ya ce hukuncin kotun kolin ya kawo zaman lafiya.

“Abin da mutum ya shuka, shi zai girba” – Kwankwaso

Ana ta yada cewa an yi sulhu tsakanin ‘yan NNPP da jam’iyyar APC kafin hukuncin kotun koli, an ji labarin matsayar Rabiu Kwankwaso.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi bayani ya ce babu wata yarjejeniya da aka yi da Bola Tinubu ko wani kafin nasarar Abba Kabir Yusuf.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng