Nasarar Kotun koli: Abin da Kwankwaso Ya Fada a Kan Abba da Yarjejeniya da APC

Nasarar Kotun koli: Abin da Kwankwaso Ya Fada a Kan Abba da Yarjejeniya da APC

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana jim kadan bayan Abba Kabir Yusuf ya yi nasara a kotun koli
  • Jagoran na NNPP ya musanya zargin yin sulhu da gwamnatin APC ko shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Kwankwaso ya ce zaben 2023 zai kasance darasi ga kowa inda aka yi tunanin APC za ta karbe mulki

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana da kotun koli ta tabbatar da nasarar Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano.

A wata zantawa da ya yi da BBC Hausa ranar Juma’a, 12 ga watan Junairu 2024, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce an koyi darasi a shari’ar.

Kwankwaso ABBA
Rabiu Musa Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Kwankwaso ya ce kowa ya dauki darasi

Kara karanta wannan

An tsame ni daga zargi, Abba Kabir ya yi godiya bayan hukuncin Kotun Koli, Ya tura sako

Jagoran na jam’iyyar NNPP a Najeriya ya ce abubuwan da su ka faru a kotuna game da shari’ar zaben 2023 darasi ne dukkanin mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A game da alakarsa da Abdullahi Umar Ganduje, madugun Kwankwasiyyan ya ce babu abin da yake ran shi da kowa sai fatan alheri.

Rabiu Kwankwaso ya ce tun da yake bai taba wani abin da zai cutar da bangaren Abdullahi Ganduje kuma yake cewa ba zai taba yi ba.

Fitaccen ‘dan siyasar yake cewa duk abin da mutum ya shuka, shi zai girba a rayuwa. Hakan ya na zuwa ne bayan Abba Yusuf ya yi nasara.

Akwai yarjeniya tsakanin APC da NNPP?

Da BBC ta tambaye sa game da alakarsa da Bola Ahmed Tinubu, ‘dan takaran na NNPP a zaben 2023 ya nuna tana nan a yadda ta ke.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun yi masifa a kan binciken da EFCC tayi a hedikwatar Dangote

Kwankwaso ya ce sun yi majalisa tare da Tinubu a 1992 kuma suka yi gwamnoni a 1999 kafin su sake haduwa bayan an kafa a APC a 2015.

Yayin da Tinubu yake jagorantar Najeriya da gwamnatinsa ta APC, Kwankwaso ya ce su kuma a gefe guda suna NNPP mai kayan marmari.

Tsohon Ministan ya musanya batun yin yarjejeniya da gwamnatin tarayya da APC kafin Abba Kabir Yusuf ya tsira da kujerarsa a kotu.

Abin da Rabiu Kwankwaso ya fada

“Ai babu abin da ba za ka ji mutane sun fada ba.
Ni dai a sani na, har yanzu ba mu zauni da wani ko wata yarjejeniyar a ba da kaza ko kar ayi kaza ba."

-Rabiu Musa Kwankwaso

Kwankwaso yake juya Abba?

Kwankwaso ya yi watsi da zargin shi yake juya gwamnan Kano, ya ce tsakaninsa da Abba sai shawara kamar sauran dubban mutanen jihar.

Kara karanta wannan

Jam’iyyun adawa sun cigaba da shirin hada kai domin yakar Tinubu da APC a 2027

‘Dan siyasar ya ce babu wanda ya isa ya juya gwamna Abba Kabir Yusuf ko wani, ya ce abin da ya kamata a duba shi ne ana aiki ko rashinsa.

Abba ya zauna da Ministar Tinubu

Ana da labari cewa Ministar kasuwanci a gwamnatin tarayya ta kai ziyara zuwa jihar Kano a ranar Alhamis, 11 ga watan Junairu 2024.

Gwamna Abba Kabir Yusuf da wasu manyan gwamnatinsa sun yi zama da Dr. Doris Anite ana shirin yanke hukunci a kan zaben jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng