Cikakkun Sunaye: Abba Yusuf, Caleb Mutfwang da Gwamnoni 8 da Kotun Koli Ta Tabbatar da Nasarorinsu

Cikakkun Sunaye: Abba Yusuf, Caleb Mutfwang da Gwamnoni 8 da Kotun Koli Ta Tabbatar da Nasarorinsu

FCT, Abuja - Takaddama da dama sun biyo bayan yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gudanar da zaben gwamna a shekarar 2023 a Najeriya.

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Fusatattun yan takara da jam'iyyun siyasa da suka yi takara a zaben watan Maris 2023 sun tunkari kotuna domin kalubalantar sakamakn zaben tare da neman gyara a kotu.

Kotun Koli da tabbatar da gwamnoni 10
Cikakkun Sunaye: Abba Yusuf, Caleb Mutfwang, da Gwamnoni 10 da Kotun Koli Ta Tabbatar da Nasarorinsu Hoto: Hoto: Abba Kabir Yusuf, Dauda Lawal, Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Ya zuwa ranar Asabar, 13 ga Janairu, 2024, gwamnoni 10 ne suka yi nasara a kotun koli, wadda ita ce ta karshe.

Ga jerin gwamnonin da Kotun Koli ta yanke hukunci a kan makomarsu a kasa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1) Hyacinth Alia (jihar Benue)

Kara karanta wannan

Kotun koli ta ƙara yanke hukunci kan sahihancin nasarar gwamnan adawa, PDP ta yi warwas

A farkon watan Janairu ne Kotun Koli ta yi watsi da daukaka karar da jam’iyyar PDP da dan takararta a zaben gwamnan Benue, Titus Uba suka yi.

Kotun ta tabbatar da zaben gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia. Alia jigo ne a jam’iyyar APC.

2) Alex Otti (jihar Abia)

A ranar Juma’a 12 ga watan Janairu ne Kotun Koli ta tabbatar da zaben Otti a matsayin gwamnan jihar Abia.

Mai shari’a Uwani Abba-Aji wacce ta karanta hukuncin da aka yanke, ta ce wadanda suka shigar da karar sun kasa tabbatar da rashin bin ka’idojin da ke cikin karar da suka daukaka.

3) Dauda Lawal (jihar Zamfara)

A ranar Juma’a, 12 ga watan Janairu, 2024, ne Kotun Koli ta tabbatar da zaben gwamna Lawal.

Babbar kotun ta yi watsi da hukuncin da ya ya kori Lawal a watan Nuwamba 2023.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta yi hukunci kan shari'ar neman tsige gwamnan APC, bayanai sun fito

4) Babajide Sanwo-Olu (Legas)

Haka kuma a ranar Juma’a, 12 ga watan Janairu, Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da zaben Babajide Sanwo-Olu a matsayin zababben gwamnan jihar Legas.

Mai shari’a Garba Lawal wanda ya karanta hukuncin ya yi watsi da karar da Gbadebo Rhodes-Vivour na jam’iyyar Labour Party (LP) ya shigar.

Haka kuma, kotun ta soke karar da dan takarar jam’iyyar PDP, Azeez Adediran (Jandor) ya shigar, inda ya nemi a tsige Gwamna Sanwo-Olu.

5) Bala Mohammed (Bauchi)

Kotun koli ta bayyana Gwamna Bala Mohammed na Bauchi a matsayin zababben gwamnan jihar.

Babbar ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Saddique Abubakar ya shigar, yana kalubalantar zaben Mohammed da kuma ayyana shi a matsayin zababben gwamnan jihar Bauchi.

6) Bassey Otu (Cross River)

Gwamna Bassey Otu na Cross River ya samu gagarumar nasara a karar da ke neman tsige shi a matsayin gwamnan jihar ta Kudu maso Kudu.

Kara karanta wannan

Bayan na Kano, Kotun Koli ta raba gardama kan shari'ar gwamnan PDP a Arewa, ta fadi dalili

A hukuncin da ta yanke a ranar Juma’a, 12 ga watan Janairu, Kotun Koli ta yi watsi da karar da PDP ta shigar.

7) Francis Nwifuru (jihar Ebonyi)

Kotun koli, a ranar Juma’a, 12 ga watan Janairu, ta tabbatar da nasarar zaben gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi.

Kotun, a hukuncin da ta yanke wanda mai shari’a Tijjani Abubakar ya zartar, ta yi watsi da kararraki guda biyu na neman korar Nwifuru na jam’iyyar APC daga mukaminsa.

8) Abba Kabir Yusuf (jihar Kano)

Kotun koli a ranar Juma’a, 12 ga watan Janairu, ta yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na tsige gwamna Yusuf na jihar Kano.

Kwamitin mutum biyar a karkashin jagorancin Mai shari’a John Okoro, sun yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na cire kuri’u 165,616 daga cikin kuri’un gwamnan Kano a zaben gwamna da aka yi a ranar 18 ga Maris, 2023.

Kara karanta wannan

Kotun Koli Ta Ayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Kano

9) Umo Eno (Akwa Ibom)

Kotun koli a ranar Alhamis, 11 ga watan Janairu, ta yi watsi da kararraki guda uku da wasu ‘yan takarar gwamna suka gabatar a gabanta na neman soke zaben gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, bisa zarginsa da gabatar da takardar bogi.

Kotu ta yi watsi da kararrakin jam’iyyun APC, Young Progressive Party (YPP) da kuma New Nigeria Peoples Party (NNPP) a wani hukunci da mamba na kwamitin kotun, Uwani Abba-Aji ya zartar.

10) Caleb Mutfwang (jihar Filato)

A daya daga cikin hukunce-hukunce da dama da aka yanke a ranar Juma’a 12 ga watan Junairu, 2024, Kotun Koli ta yanke hukuncin da aka dade ana jira a kan rikicin zaben gwamnan jihar Filato.

Kotun kolin ta tabbatar da zaben Caleb Mutfwang, inda ta kara tabbatar da cewa shi ne zababben gwamnan jihar Filato.

Abba ya magantu kan Tinubu da Shettima

A wani labarin kuma, mun kawo cewa a halin yanzun dai kotun kolin Najeriya ta binne duk wata taƙaddama kan zaben gwamnan jihar Kano da aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Jaridar Vanguard tace Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da mataimakinsa, Ƙashim Shettima ba su tsoma baki a shari'ar Kano ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng