Jam’iyyun Adawa Sun Cigaba da Shirin Hada Kai Domin Yakar Tinubu da APC a 2027

Jam’iyyun Adawa Sun Cigaba da Shirin Hada Kai Domin Yakar Tinubu da APC a 2027

  • Wasu 'yan adawa sun fara amsa kiran Atiku Abubakar na hada-kai domin a karbe mulki a Najeriya
  • Watakila ayi taron dangi da nufin ganin bayan Bola Tinubu a zaben shugaban kasa da za ayi a 2027
  • Alamu sun nuna zai yi wahala idan kan ‘yan adawa ya rabu su iya tunkarar jam’iyyar APC mai-ci

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Jam’iyyun hamayya a Najeriya sun soma cigaba da tattaunawa a kan yadda za su dunkule domin yakin zabe mai zuwa.

Daily Trust ta ce ‘yan adawan su na so su hada-kai kafin zaben shugaban kasa a 2027.

Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Tarihin yunkurin yi wa APC taron dangi

Tun a 2021, wasu jagororin hamayya su ka fara wannan yunkurin da bai yi nasara ba, a karshe Bola Ahmed Tinubu ya lashe zabe.

Kara karanta wannan

Wasu ‘yan jam’iyyar PDP da ke goyon bayan Gwamnatin Tinubu a boye ko a zahiri

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin wadanda su ka fara kokarin ganin an dunkule akwai Farfesa Pat Utomi da Ghali Na’Abba wanda ya rasu kwanan nan.

A cikinsu har da Dr. Hakeem Baba Ahmed wanda ya shiga gwamnati da Farfesa Kingsley Moghalu da Marigayi Dr. Obadiah Mailafia.

Ko a zaben 2019, Dr. Thomas Wilson-Ikubese Omoyele Sowore, Fela Durotoye da Adamu Garba sun nemi yin hakan, ba a dace ba.

Nasarar APC da Tinubu a kotu

Jim kadan bayan nasarar Bola Ahmed Tinubu a kotun koli, sai jagororin adawa su ka dawo da maganar dunkulewa a inuwa guda.

Jagoran hamayya a Najeriya, Atiku Abubakar wanda yayi takara a PDP ya yi kira da a hada-kai Peter Obi da su Rabiu Kwankwaso.

Wazirin Adamawa ya nuna sai da taron dangi ne kurum za a iya kifar da mulkin APC.

Kara karanta wannan

Hadiman Atiku 5 da su ka juya masa baya, suka yi aiki da Gwamnati da APC

Watakila a hada-kai a kan APC

Masana da masu fashin baki sun nuna idan har ana so a doke APC a zaben shugaban kasa a 2027, dole sai an yi mata taron dangi.

Babu mamaki idan NNPP ta rasa jihar Kano a kotun koli, hakan ya kawo karshen kawancen da ke tsakanin jam’iyyar da APC.

Shirye-shiryen jam'iyyar APC

A gefe guda, jam’iyyar APC ta bakin shugabanta watau Abdullahi Umar Ganduje ta ce burinta shi ne ta karbe karin jihohi da kujeru.

Abdullahi Ganduje ya ce APC na harin wasu jihohi da kujerun 'yan majalisa wanda yanzu su na hannun jam'iyyun hamayya ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng